Kano: Siyasar Abba Ta Ƙara Samun Matsala, Magoya Bayansa Sun Koma Tafiyar APC

Kano: Siyasar Abba Ta Ƙara Samun Matsala, Magoya Bayansa Sun Koma Tafiyar APC

  • A yayin da siyasar Kano ke cigaba da ɗaukan sabon salo, wasu magoya bayan Abba Kabir Yusuf sun sauya sheƙa daga NNPP
  • Matasan da suka kasance ƴaƴan jam'iyyar NNPP sun koma tafiyar Abdullahi Umar Ganduje a jam'iyyar APC mai mulki
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karɓi matasan a birnin tarayya Abuja a jiya Litinin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tafiyar siyasar gwamnan jihar Kano Abba Kabir ta kara da samun tangarɗa a jiya Litinin.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rasa wasu magoya bayansa da suka sauya sheka zuwa jami'yyar APC.

Sauya sheka
Yan NNPP sun sauya sheka a Kano. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Sanata Barau Jibrin ne ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ƴaƴan jam'iyyar NNPP sun dawo tafiyar APC a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 na cikin matsala, Ganduje ya jero jihohin da APC za ta ƙwace a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran NNPP ya dawo APC a Kano

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa babban jagoran NNPP a karamar hukumar Shanono Adamu Ciroma Koya ya dawo APC.

Malam Adamu Ciroma Koya ya dawo tafiyar jami'yyar APC ne tare da wasu tawagar matasan jam'iyyar NNPP da suka cire jar hula.

APC za ta girmama Ciroma Koya

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya mika godiya ga dukkan waɗanda suka sauya shekar.

Barau Jibrin ya kuma ba su tabbacin cewa jami'yyar APC za ta karramasu wajen yin aiki da su tare a cikin dukkan ayyukanta.

Kokarin gwamnatin APC kan tsadar abinci

Har ila yau, Sanata Barau Jibrin ya bayyana masu irin kokarin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake wajen kawo mafita ga Najeriya.

Saboda haka ya bukacesu da su cigaba da marawa shugaban kasa baya wajen ganin an samu nasara a tafiyar.

Kara karanta wannan

Sukar Shugaba Tinubu ta jawo sanatan Arewa na fuskantar barazana a zaben 2027

An biya yan fansho a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ƙaddamar da shirin biyan kuɗaɗen giratuti kashi na biyu a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da biyan kuɗin waɗanda sun kai Naira biliyan 5 daga shekarar 2016 zuwa 2019.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng