"Ya na Batawa Kansa Lokaci ne," Tsagin NNPP ya Zargi Kwankwaso da Makircin Kwace Jam'iyya

"Ya na Batawa Kansa Lokaci ne," Tsagin NNPP ya Zargi Kwankwaso da Makircin Kwace Jam'iyya

  • Tsagin NNPP mai adawa da Rabiu Kwankwaso ya zargi tafiyar Kwankwasiyya da kokarin karbe masu jam'iyya ta hanyar sauya tambarinta
  • Sakataren jam'iyyar na kasa, Oginni Olaposi Sunday ne ya yi zargin, inda ya ce ba za su amince ba kuma sun shigar da kara gaban kotu
  • Sunday na wannan zargi ne a sa'ilin da dan takarar shugaban kasa a 2023, Rabi'u Kwankwaso ya ce ba mai korarsa daga cikin NNPP

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT, Abuja - Tsagin NNPP ya zargi dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso da kokarin kwace jam'iyyar. Sakataren jam'iyyar na kasa, Oginni Olaposi Sunday ya ce sauya tambarin NNPP da mika shi ga hukumar zabe (INEC) da Sanata Kwankwaso ya yi bata lokaci ne kawai.

Kara karanta wannan

"Muna maraba da kai": Kwankwaso ya tura sakon gayyatar El Rufai zuwa NNPP a bidiyo

Kwankwaso
Tsagin NNPP ya zargi Sanata Kwankwaso da yunkurin kwace masu jam'iyya Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Oginni ya kara da zargin tafiyar Kwankwasiyya da hada baki da jami'an INEC wajen kwace masu jam'iyya.

"NNPP mai bin doka ce" - Sunday

Sakataren jam'iyyar NNPP na kasa, Oginni Olaposi Sunday ya ce su masu bin doka da oda ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Sunday ya ce yanzu haka sun shigar da kara kotu su na kalubalantar Rabi'u Musa Kwankwaso da sauya tambarin jam'iyyar.

Ya ce Dr Boniface Okechukwu Aniebonam ne ya kafa ta shekaru 22 da su ka shude, kuma ba za su bari Kwankwaso ya kwace ta ba.

"INEC ba ta kyauta ba." Inji Tsagin NNPP

Tsagin NNPP mai adawa da Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa hukumar INEC, karkashin Farfesa Mamoud Yakubu ba ta kyauta masu ba.

Ya ce bai kamata a hada baki da su wajen sauya tambarin jam'iyyar ba, inda ya ce abin da ya fi dacewa shi ne su kafa ta su jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Sabuwar tafiya: Hotunan yadda Kwankwaso ya kaddamar da sabon tambarin NNPP a Abuja

"Babu mai kora ta daga NNPP," Kwankwaso

A baya mun kawo labarin cewa dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce babu mai iya korarsa daga NNPP.

Sanata Kwankwaso ya ce a matsayinsa na halastaccen dan jam'iyya da ya taka muhimmiyar rawa wajen daukaka ta, ya na nan daram.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.