Sarautar Kano: Kwankwaso Ya Fadi Dalilin Tuge Aminu Ado, Ya Ce Zuga Shi Ake Yi

Sarautar Kano: Kwankwaso Ya Fadi Dalilin Tuge Aminu Ado, Ya Ce Zuga Shi Ake Yi

  • Yayin da ake ci gaba rigimar sarautar Kano, Sanata Rbiu Kwankwaso ya bayyana musabbabin tuge Aminu Ado Bayero
  • Kwankwaso ya ce Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya dauki matakin ne saboda cika alkawuran kamfe da ya dauka
  • Tsohon gwamnan Kano ya koka kan yadda ake zuga Aminu Ado duk da tun farko ya amince da hukuncin da aka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan rigimar sarautar Kano bayan mayar da Muhammadu Sanusi II.

Kwankwaso ya ce daukar matakan da Abba Kabir ya yi game da masarautun cika alkawuran kamfe da ya dauka ne.

Kwankwaso ya fadi musabbabin tuge Aminu Ado daga jihar Kano
Sanata Rabiu kwankwaso ya magantu kan rigimar sarautar Kano. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

Kwankwaso ya ce zuga Aminu Ado ake

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kwankwaso, Abba sun sake shiga matsala kan zargin rubuta wasika

Tsohon gwamnan kano ya bayyana haka ne yayin wata hira da 'yan jaridu, kamar yadda The Nation ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Kwankwaso ya zargi wasu a Abuja da zuga Aminu Ado Bayero domin dawowa Kano bayan tube shi a sarauta.

Ya ce suna zuga shi duk da shi da sauran sarakuna hudu da aka tube a lokacin sun riga sun amince da hukuncin da aka yi, cewar Daily Post.

Kwankwaso ya fadi musabbabin tube Aminu Ado

"Wannan duk yana daga cikin alkawuran kamfen ne, ka da ka manta an mayar da Sanusi II a shekarar 2014."
"Mataimakina da ya zama gwamna ya yanke shawarar raba masarautun Kano gida hudu wanda an taba gwada yin haka a mulkin Rimi."
"Wannan ita ce matsayarmu dawo da masarautun daya, a lokacin kamfe gwamnan ya zaga inda yake yiwa mutanen Kano alkawarin dawo da masarauta daya idan suka zabe shi."

Kara karanta wannan

Sanata ya bayyana abin da yasa Tinubu ya gagara shawo kan tsadar abinci

- Sanata Kwankwaso

Kwankwaso ya ce a shekara daya gwamna ya dauki matakin sauya tsarin masarautu inda yabi duka tsarin da ya kamata ta hanyar Majalisa.

Kwankwaso ya gayyaci El-Rufai zuwa NNPP

Kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP a bude take ga dukkan wanda yake son shigowa.

Kwankwaso musamman ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai tayi zuwa jam'iyyar NNPP.

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana musabbabin sauya tambarin jam'iyyar da cewa sun fusknaci matsala a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.