"Muna Maraba da Kai": Kwankwaso Ya Tura Sakon Gayyatar El Rufai Zuwa NNPP a Bidiyo
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP budaddiya ce ga kowa
- Kwankwaso ya ce idan har tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai yana son shigowa jam'iyyar to suna yi masa maraba da zuwa
- Sanatan ya kuma bayyana amfanin sauya tambarin jam'iyyar da launinta bayan samun matsaloli a zaben shekarar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan bude kofa da suka yi ga duk mai son shiga jam'iyyar NNPP.
Kwankwaso ya ce suna maraba da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai idan zai shigo jam'iyyar.
Kwankwaso ya yiwa El-Rufai tayin NNPP
Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne a cikin wata hira a faifan bidiyo da BBC Hausa ta wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya ce jam'iyyar NNPP a bude take ga kowa da ke son shigowa har da tsohon gwamna, Mallam Nasiru El-Rufai.
Kwankwaso ya kuma bayyana dalilin sauya tambarin jam'iyyar inda ya ce sun ci karo da matsaloli a zaben 2023.
"Ita jam'iyya a bude take, Malam Nasiru El-Rufai idan zai shigo muna yi masa maraba da zuwa."
"Haka kuma kowane ɗan Najeriya yana da dama ya shigo jam'iyyar kamar yadda yake da damar fita."
- Rabi'u Kwankwaso
"Musabbabin sauya tambarin NNPP" - Kwankwaso
Ya ce babu kamshin gaskiya kan zargin wai rikicin cikin gida ne musabbabin sauya tambarin jam'iyyar.
Sanatan ya ce musabbabin bai rasa nasaba da matsalolin da suka fuskanta wurin gane jam'iyyar a takardar kuri'a a zabe.
Kwankwaso ya magantu kan korarsa a NNPP
A wani labarin, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce har yanzu su ne halastattun ƴan jam'iyyar.
Sanata Kwankwaso ya ce kuma sun koma jam'iyyar domin samar da kyakkyawar manufa ta ceto Najeriya da ƴan ƙasar.
Ya bayyana cewa babu wanda ke da ikon korarsa daga jam’iyyar da suka raya har ta kai ga matakin da ta ke a yanzu.
Asali: Legit.ng