Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Korarsa a NNPP, Ya Fadi Matsalar da Suka Fuskanta a Zabe

Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Korarsa a NNPP, Ya Fadi Matsalar da Suka Fuskanta a Zabe

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan korarsa da aka yi a jam'iyyar NNPP inda ya ce babu wanda ya isa
  • Kwankwaso ya ce har yanzu su halastattun ƴan jam'iyyar ne wanda suka ba da gudunmawa sosai har ta kawo war haka
  • Tsohon gwamnan ya kuma yi fatali da jita-jitar cewa rikicin cikin gida ne ya saka su sauya tambarin jam'iyyar daga kayan marmari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce har yanzu su ne halastattun ƴan jam'iyyar.

Sanata Kwankwaso ya ce kuma sun koma jam'iyyar domin samar da kyakkyawar manufa ta ceto Najeriya da ƴan ƙasar.

Kara karanta wannan

Babban jigo kuma tsohon kakakin kamfen Atiku Abubakar ya sauya sheƙa daga PDP

Kwankwaso ya bugi kirji kan gudunmawa da ya ba NNPP
Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi fatali da maganar korarsa a jam'iyyar NNPP. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

Kwankwaso ya fadi gudunmawarsa ga NNPP

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne yayin martani kan ikirarin korarsa a jam'iyyar, kamar yadda BBC Hausa ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa babu wanda ke da ikon korarsa daga jam’iyyar da suka raya har ta kai ga matakin da ta ke a yanzu.

"A ganinmu waɗannan mutane ba yan siyasa bane, ba su fahimci yadda tsarin yake ba, ni ba shugaba bane kawai na Kano, ni ne jagoran wannan jam'iyya a Najeriya."
"Lallai ana son kowa ya shigo wannan jam'iyya, ba za a ce ba a so wani ya shigo ba, wannan jam'iyya ba ta kowa bace, ta ƴan ƙasa ce."

- Rabi'u Kwankwaso

Kwankwaso ya fadi dalilin sauya tambarin NNPP

Kwankwaso ya yi magana kan sauya tambarin jam'iyyar da suka yi inda ya bayyana amfanin hakan ga hadin kan ƴan jami'yyar.

Kara karanta wannan

Fashin magarkama: 'Yan Boko Haram sama da 100 sun tsere daga gidan yarin Nijar

Ya ce babu kamshin gaskiya kan zargin wai rikicin cikin gida ne musabbabin sauya tambarin jam'iyyar.

Sanatan ya ce musabbabin bai rasa nasaba da matsalolin da suka fuskanta wurin gane jam'iyyar a takardar kuri'a a zabe.

Kungiya ta gargadi Kwankwaso da Abba Kabir

Kun ji cewa wata ƙungiyar a Arewacin Najeriya ta yi magana kan zargin Rabiu Kwankwaso da rubuta wasika ga ƴan Majalisun Tarayya.

Ana zargin Kwankwaso ya rubuta wasikar ga ƴan Majalisa domin yin bore ga Bola Tinubu kan Rigimar masarautu a jijar a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.