Ka Zo a Zauna: Jigon PDP Ya Nemo Hanyar Sasanta Fubara da Wike, Ya Sanya Atiku a Ciki

Ka Zo a Zauna: Jigon PDP Ya Nemo Hanyar Sasanta Fubara da Wike, Ya Sanya Atiku a Ciki

  • An bukaci jiga jigan PDP su saka hannu wajen kawo ƙarshen rikicin da ya barke tsakanin Siminalayi Fubara da Nyesom Wike
  • Wani ƙusa a jami'yyar PDP, Dakta Tom Fredfish ne ya yi kiran yana mai cewa abin kunya ne ace ga manya amma sun gaza tabuka komai
  • Dakta Tom Fredfish ya yi kiran ne bayan ganin rikicin ya dauki kimanin shekara daya amma ba a hango alamar zai kawo karshe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - 'Yan jami'yyar PDP sun fara korafi kan gaza magance rikicin gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike.

Wani ƙusa a jami'yyar, Dakta Tom Fredfish ya bukaci manya a tafiyar PDP su gaggauta daukan matakin kawo karshen rikicin.

Kara karanta wannan

Yobe: 'Yan sanda sun cafke basarake bisa zargin hannu a kisan wani bawan Allah

Fubaran da Wike
An bukaci manyan jam'iyya su shiga tsakanin Fubara da Wike. Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Ezonwo Wike
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Dakta Tom Fredfish ya bukaci irinsu Atiku Abubakar da Sanata Adolphus Wabara su saka baki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike vs Fubara: Abin da Atiku zai yi

Dakta Tom Fredfish ya ce ana rikicin jam'iyya irin wannan bai kamata ace jigo irin Atiku Abubakar ya tsaya a tsakiya ba.

A cewar Dakta Tom, ya kamata ace Atiku Abubakar ya fito ya nuna yatsa domin kawo karshen rikicin, rahoton Business Day.

Haka zalika ya yi kira ga shugaban kwamitin amintattun jami'yyar, Sanata Adolphus Wabara kan daukan mataki domin kawo karshen rikicin.

Dakta Tom: 'PDP na buƙatar haɗin kai'

Dakta Tom Fredfish ya nuna takaici kan yadda jam'iyyar PDP ta gaza samun hadin kai a wannan lokacin.

Tom Fredfish ya bayyana cewa hadin kai da adalci ne taken jami'yyar PDP amma an gagara dunkulewa wuri ɗaya.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya fara samun koma baya, shugabannin NNPP sun koma APC

A karshe, Dakta Tom ya ce bai kamata shugabannin PDP su rika sukan gwamnatin APC ba matuƙar sun gaza samar da mafita a jihar Rivers.

Fubara vs Wike: Shehu Sani ya yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers mai arziƙin man fetur wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya bayyana cewa Allah ne kaɗai zai iya sasanta tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng