Tiga: Ba a Gama da Rigimar Sarauta Ba, Sanata Ya Bukaci Kirkirar Sabuwar Jiha a Kano
- Yayin da ake gasar kirkirar sababbin jihohi a Najeriya, sanatan Kano ya kawo sabon kudiri gaban Majalisar Tarayya
- Sanata Kawu Sumaila da ke wakiltar Kano ta Kudu ya gabatar da kudirin kirkirar sabuwar jiha a Kano
- Sabuwar jihar idan kudirin ya tabbata za ta fito ne daga Kano wanda aka sanyawa suna 'Jihar Tiga'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya gabatar da kudiri a Majalisar Tarayya.
Sanata Sumaila ya gabatar da kudirin ne domin neman kirkirar sabuwar jiha a Kano.
Kano: Sanata ya bukaci kirkirar sabuwar jiha
Dan Majalisar ya gabatar da kudirin me a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024 yayin zamanta a Abuja, kamar yadda @Imranmuhdz ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabuwar jihar da ake neman kirkira mai suna 'Tiga' za a balle ta ne daga jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.
Kudirin da sanatan ya gabatar ya tsallake karatu na daya a Majalisar wanda zai yi sanadin raba jihar Kano gida biyu, cewar Daily Post.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigima kan masarautun Kano tsakanin Aminu Ado da Sanusi II.
Kokarin kirkirar sababbin jihohi a Najeriya
Wannan na zuwa ne yayin da wasu ƴan Majalisun Kudancin Najeriya ke neman kirkirar jihohi a yankunansu.
Sanata Ned Nwoko daga jihar Delta ya gabatar da kudirin neman ƙirƙirar sabuwar jihar Anioma a yankin Kudu maso Gabashin kasar.
Nwoko ya ce hakan zai ba yankin da ke da jihohi biyar damar shiga sahun sauran yankuna da ke da jihohi shida a ƙasar.
Har ila yau, Sanata Osita Izunaso ya gabatar da kudirin kirkirar sabuwar jihar Orlu a yankin Kudu maso Gabas.
Daga bisani wasu ƴan Majalisu sun gabatar da kudiri domin kirkirar karin jiha daga Lagos a kudancin Najeriya.
Sababbin jihohi da ke son kirkira a Najeriya
Kun ji cewa tun farkon hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki, Majalisar Dattawa take ta kokarin ganin da kawo canji a kudin tsarin mulki.
Daga cikin manyan sauye-sauyen da ake so a yi a kundin, akwai yunkurin kirkirar sababbin jihohi a yankun Kudancin kasar nan.
Asali: Legit.ng