Shehu Sani Ya Bayyana Wanda Zai Kawo Karshen Rikicin Gwamna Fubara da Wike
- Sanata Shehu Sani ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers mai arziƙin man fetur wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa
- Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya bayyana cewa Allah ne kaɗai zai iya sasanta tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa Nyesom Wike
- Gwamna Fubara da Wike dai sun daɗe suna takun saƙa tun bayan da aka rantsar da Fubara a matsayin gwamnan jihar a shekarar 2023
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan rikicin siyasar da ke tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike.
Shehu Sani ya bayyana cewa Allah ne kaɗai zai iya magance rikicin siyasar da ke tsakanin mutanen biyu waɗanda ba sa ga maciji da juna a halin yanzu.
Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, a ranar Talata, 9 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Shehu Sani ya ce kan rikicin Fubara da Wike?
Shehu Sani ya nuna cewa a yanzu an zurawa sarautar Allah ido kan rikicin siyasan wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
"An bar jihar Rivers a hannun Allah domin magance matsalar."
Idan ba a manta ba dai jihar Ribas ta tsinci kanta cikin rikicin siyasa tun bayan hawan Gwamna Siminalayi Fubara.
Gwamna Fubara da Wike dai na rikici ne a kan wanda zai yi ikon siyasa a jihar.
Rikicin ya haifar da ɓallewar majalisar dokokin jihar zuwa gida biyu, inda Martin Amaewhule da Victor Oko-Jumbo ke jagorantar kowane ɓangare.
Ƙoƙarin shiga tsakanin da Shugaba Bola Tinubu ya yi tun da farko bai haifar da sakamakon da ake tsammani ba, domin magoya bayan Wike da Gwamna Fubara sun ci gaba da takalar juna faɗa.
Gwamna Fubara zai binciki Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya sha alwashin kafa kwamitin bincike da zai binciki tsohuwar gwamnatin Nyesom Wike da ta shuɗe kafin ya hau mulki.
Simi Fubara ya bayyana hakan ne yayin rantsar da Dagogo Israel Iboroma, SAN, a matsayin Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a a gidan gwamnati da ke Port Harcourt.
Asali: Legit.ng