"Babu Wanda Ya San Kwankwaso": APC Ta Fadi Illar da NNPP Za Ta Samu a Zaɓen 2027
- Jami'yyar APC a jihar Kano ta yi martani kan maganganun NNPP a jihar game da barazana da Bola Tinubu ke fuskanta
- APC ta ce rigimar sarautar Kano babu abin da za ta yiwa Tinubu sai dai ma ta jawowa NNPP matsala saboda nuna bangaranci
- Shugaban jam'iyyar a jihar, Abdullahi Abbas shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin 8 ga watan Yulin 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi martani mai zafi ga NNPP.
Abbas ya ce jam'iyyar NNPP za ta sha kashi a zaben 2027 saboda yadda ta nuna bangaranci a rigimar sarautar Kano.
Kano: APC ta yi martani ga NNPP
Shugaban APC ya bayyana haka ne a jiya Litinin 8 ga watan Yulin 2024 a cikin wata sanarwa, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abbas ya ce madadin rusa damar Bola Tinubu a zaben 2027, NNPP ce za ta samu matsala saboda dambarwar sarauta a jihar.
Ya ce Rabiu Kwankwaso ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba saboda ba shi da goyon bayan jama'ar kasa baki daya, Daily Trust ta tattaro.
APC ta fadi lissafin zaben 2023
"Kwankwaso ya samu kuri'u 1,454,649 ne kadai da bai wuce 6.23% ba kuma mafi yawansu daga Kano."
"Dadi da kari, bayan zabe rahotanni sun tabbatar da cewa Kwankwaso bai samu sama da kuri'u 100,000 ba bayan jihar Kano."
"Ta yaya Peter Obi da ya fito daga Kudu maso Gabas zai fi Kwankwaso samun kuri'u a jihohin Arewa guda 13?"
"Jihohin sun hada da Kaduna da Taraba da Borno da Gombe da Kebbi da Kogi da Kwara da Niger da Sokoto da Nasarawa da Plateau da Adamawa da Benue."
- Abdullahi Abbas
NNPP ta gargadi Tinubu kan rigimar Kano
Kun ji cewa jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta gargadi Shugaba Bola Tinubu kan matsayarsa a rigimar sarautar Kano.
Shugaban jam'iyyar a jihar, Hashimu Dungurawa shi ya bayyana haka inda ya ce matsalar za ta shafi zaben Tinubu a 2027.
Asali: Legit.ng