Jam'iyyar NNPP Ta Bayyana Matsayarta Kan Dakatar da Gwamna Abba da Korar Kwankwaso

Jam'iyyar NNPP Ta Bayyana Matsayarta Kan Dakatar da Gwamna Abba da Korar Kwankwaso

  • Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta yi fatali da dakatarwar da wani tsaginta ya yiwa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf
  • Jam'iyyar ta kuma yi fatali da korar da aka yiwa jagoranta na ƙasa kuma ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Shugaban jam'iyyar na jihar, Hashim Dungurawa, ya bayyana matakin dakatarwar da korar a matsayin haramtacce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta yi watsi da matakin dakatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar da wani tsagin kwamitin zartaswar jam’iyyar na ƙasa ya yi.

Jam'iyyar ta bayyana matakin na dakatar da Gwamna Abba a matsayin haramtacce.

NNPP ta yi watsi da korar Kwankwaso daga jam'iyyar
Jam'iyyar NNPP reshen Kano ta yi watsi da korar Gwamna Abba daga jam'iyyar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: An aika gargadi ga Kwankwaso da jam'iyyar NNPP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me NNPP ta ce kan korar Kwankwaso?

Jam’iyyar ta kuma yi watsi da korar da aka yiwa jagoranta kuma ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Kwankwaso, wacce tsagin ya yi.

NNPP ta bayyana dakatarwar a matsayin abin dariya, inda ta dage cewa wasu korarrun ƴaƴan jam’iyyar NNPP ne suka aikata hakan, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ya kuma yi zargin cewa wasu ne suka ɗauki nauyin waɗanda suka dakatar da Gwamna Abba tare da korar Kwankwaso daga jam'iyyar.

Dungurawa ya bayyana batun dakatarwar da korar a matsayin abin rashin hankali wanda ba zai yi tasiri ba a kan jam'iyyar.

An dakatar da Abba daga NNPP?

Ya yi mamakin yadda wasu korarrun ƴaƴan jam'iyyar za su dakatar da Gwamna Abba.

'Dan siyasar ya ce Abba shi ne kaɗai gwamnan NNPP a ƙasar nan da jagoranta na ƙasa inda ya bayyana hakan a matsayin shirme.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: An fadi matsalar da Tinubu zai samu a Kano a siyasa

An gargaɗi jam'iyyar NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Progressive Front of Nigeria (ProFN) ta yi Allah wadai da jam'iyyar NNPP da shugabanninta bisa yin ƙage kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ƙungiyar na yin martani ne kan zargin da shugaban jam'iyyar na jihar Kano ya yi na cewa shugaba Tinubu na da hannu a rikicin masarautar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng