Atiku, Obi, Kwankwaso: Kungiya Ta Faɗi Ɗan Takarar da Zai Iya Ƙwace Mulki Hannun APC

Atiku, Obi, Kwankwaso: Kungiya Ta Faɗi Ɗan Takarar da Zai Iya Ƙwace Mulki Hannun APC

  • Kungiyar matasa masu goyon bayan Atiku Abubakar (NYFA) ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ne kadai zai iya kwace mulki
  • Kungiyar NYFA ta yi kira ga 'yan Najeriya da su zabi Atiku Abubakar a 2027 domin gyara tattalin arziki da kuma ci gaban kasa
  • Kakakin kungiyar, Dare Dada ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi inda ya fadi wasu manufofin Atiku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wata kungiyar matasa magoya bayan Atiku, NYFA, ta bukaci ‘yan Najeriya da su goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2027.

Kungiyar NYFA ta ce ta yi "wannan kiran ne bisa imanin cewa shi ne dan takara daya tilo da zai iya kwace mulki daga hannun APC."

Kara karanta wannan

2027": NNPP ta gargaɗi Tinubu kan rigimar Kano, ta shirya sake gwada Kwankwaso

Kungiyar NYFA ta yi magana kan takarar Atiku a 2027
Kungiyar NYFA ta ce Atiku ne kadai zai iya karbar mulki hannun APC a 2027. Hoto: @atiku, @PeterObi, @officialABAT
Asali: Facebook

"Atiku zai gyara tattalin Najeriya" - NYFA

Kakakin kungiyar, Dare Dada, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya ce sun yi amanna da cewa Wazirin Adamawa zai kawo sauyi ga al’umma, inji rahoton Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dare Dada ya ce mulkin Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya zai kawo karshen matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi.

Ya ce dole ne al’umma su tashi tsaye wajen zabawa kansu shugaban da zai cire masu kitse a wuta tare da nuna adawa da tsare-tsaren da ke yin illa ga ci gaban al’umma.

NYFA: "Atiku zai kara karfin jihohi"

Jaridar PM News ta ruwaito Mista Dada ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a 2023 ya kasance mutum wanda bai nuna bambanci ga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ina za su saka kansu?" Atiku ya magantu kan karuwar garkuwa da mutane

Ya ce Atiku Abubakar yana da gogewa a harkokin kasuwanci da mulkin jama’a, wanda zai tafiyar da al’amuran kasar nan yadda ya kamata.

A cewar kungiyar NYFA, Atiku ya yi imanin cewa akwai bukatar karawa jihohi da kananan hukumomi karfin iko, “domin tsarin da ake tafiya kan shi a yanzu ba zai kawo ci gaba ba."

Tattaunawar Atiku-Obi ta je kunnen APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa hankalin jam’iyyar mai mulki ta APC ya fara karkata kan tattaunawar hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi.

Ana rade-radin cewa jagororin biyu na saka labule ne domin tattaro dabarun kwace mulkin kasar nan daga hannun shugaba Bola Ahmed Tinubu a kakar zaben 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.