2027: NNPP Ta Gargaɗi Tinubu Kan Rigimar Kano, Ta Shirya Sake Gwada Kwankwaso
- Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, shugaban NNPP a jihar ya tura roko ga Shugaba Bola Tinubu kan matsalar
- Hashimu Dungurawa ya bayyana yadda matsayar Tinubu a rigimar za ta kawo masa matsala a zaben 2027 da ake tunkara
- Dungurawa ya bukaci shugaban kasar da ya yi duk mai yiwuwa wurin dakile matsalar tun kafin ta wuce gona da iri
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Hashimu Dungurawa ya yi tsokaci kan rigimar sarautar jihar.
Dungurawa ya ce rashin tsoma bakin Bola Tinubu a rigimar zai iya kawo masa cikas a zaben 2027 da ake fuskanta.
Sarautar Kano: NNPP ta shawarci Tinubu
Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne ga manema labarai a yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yadda Tinubu ya nuna matsayarsa kan rigimar da ke faruwar zai yi matukar tasiri a zabensa na 2027, Leadership ta tattaro.
"A tunaninsa matsayarsa kan rigimar sarautar Kano zai yi masa amfani a 2027 bai sani ba sai lokaci ya kure zai gane ya tafka babban kuskure."
- Hashimu Dungurawa
Dungurawa ya bukaci Tinubu da yi amfani da fikirarsa wurin kawo karshen rigimar da ake yi.
Ya kuma roke shi da ya yi mai yiwuwa domin fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga jihar.
2027: NNPP ta shirya tsayar da Kwankwaso
Shugaban NNPP ya ce sun shirya tsaf wurin sake tsayar da Sanata Rabiu Kwankwaso a zaben 2027 mai zuwa.
"Za mu sake tsayar da Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2027."
"Saboda a yanzu shi ne ɗan takara da zai iya tabuka wani abu da kuma zai iya kasancewa shugaban kasa da yardar Allah."
- Hashimu Dungurawa
Sarautar Kano: Buba Galadima ya gargadi Tinubu
Kun ji cewa jigon jami'yyar NNPP, Buba Galadima ya gargadi Bola Tinubu kan rigimar sarautar Kano da ake ciki.
Galadima ya ce yadda Tinubu ke wasa da rigimar sarautar jihar zai iya zama matsala ga siyasarsa musamman a zaben 2027.
Asali: Legit.ng