Jigon APC Ya Cika Baki, Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yiwa Tinubu a 2027

Jigon APC Ya Cika Baki, Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yiwa Tinubu a 2027

  • Jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bayyana cewa ƴan Najeriya za su sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Nze Chidi Duru ya bayyana cewa sauye-sauyen da ake yi kan tattalin arziƙin ƙasar nan sun zama dole ne domin farfaɗo shi daga durƙushewa
  • Akwai masu fargabar cewa shugaban ƙasan ba zai kai labari ba a 2027 saboda halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta bayyana ra’ayin cewa za a sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu a shekarar 2027 duk da matsalar tattalin arziƙi da kuma shirin ƙawance tsakanin manyan jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan yiwa 'yan NYSC karin alawus

Matsin tattalin arziƙi sakamakon sauye-sauyen da ake yi kamar cire tallafin man fetur ya haifar da fargabar cewa ƴan Najeriya na iya ƙin zaɓen Tinubu a 2027.

Jigon APC ya ce za a sake zaben Tinubu
Jigon APC ya ce 'yan Najeriya za su sake zaben Tinubu a 2027 Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Sai dai mataimakin sakataren tsare-tsare na ƙasa na APC, Nze Chidi Duru, a wata hira da jaridar The Punch, ya ce dole ne a fara aiwatar da sauye-sauyen da ake yi domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan wanda ke neman durƙushewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me jigon APC ya ce kan sake zaɓen Tinubu?

Ya bayyana cewa jam'iyyar APC tana sane da matsin tattalin arziƙin da ake ciki a halin yanzu a ƙasar nan.

"Lokacin da shugaban ƙasa ya hau mulki, ya buƙaci ƴan Najeriya kada su tausaya masa. Muƙami ne wanda ya nema kuma ya yi aiki tuƙuru wajen samu domin shugabantar Najeriya."
"Abin da ke ba ni ƙwarin gwiwa shi ne cewa shugaban ƙasa yana sane da tsammanin mutumin da ke kan titi. Mafi ƙarancin tsammanin shi ne suna buƙatar samun kwanciyar hankali."

Kara karanta wannan

Ana batun yarjejeniyar samoa, Tinubu ya fadi abin kunyar da Najeriya ta yi

"Saboda haka haka tattaunawar da ake yi kan zaɓen 2027 ba za ta ƙare ba. A rayuwar ƙasa, shekara huɗu kamar jiya ne."
"Dangane ne da batun ko za a sake zaɓen mu, a matsayin ɗan dimokuraɗiyya kuma bisa ra'ayina, mun sha faɗin cewa idan dai har ba Shugaba Tinubu ne ya ce ba zai yi takara ba, shi ne zai wakilci APC a 2027."

- Nze Chidi Duru

Jigon PDP ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jam'iyyar PDP a Najeriya, Abdul-aziz Na'ibi Abubakar ya yi tsokaci kan zaben 2027 da ƴan Arewa.

Abdul-aziz ya ce Bola Tinubu ba zai taba samun ƙuri'un ƴan Arewa ba musamman bayan sanya hannu a kan yarjejeniyar Samoa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng