Bayan Rigimar Aurar da Marayu a Niger, Ɗan Majalisa Ya Kinkimo Auren Mata 105

Bayan Rigimar Aurar da Marayu a Niger, Ɗan Majalisa Ya Kinkimo Auren Mata 105

  • Yayin da ta'addanci ya yi ajalin iyaye a jihar Zamfara, dan Majalisar Tarayya ya tallafawa marayu a jihar
  • Abdulmalik Zubairu da ke wakiltar Bungudu/Maru ya dauki nauyin auren mata marayu 105 wadanda iyayensu suka rasa rayukansu
  • Ɗan Majalisar ya ce ya yi hakan ne domin dauke musu nauyin wahalar hidimar aure ganin cewa ba su da iyaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Dan Majalisar Tarayya daga jihar Zamfara ya dauki nauyin aurar da mata marayu 105 a jihar.

Hon. Abdulmalik Zubairu da ke wakiltar mazabar Bungudu/Maru ya dauki matakin domin tallafawa matan wadanda ƴan bindiga suka hallaka Iyayensu.

Dan Majalisa ya aurar da mata marayu 105va Zamfara
Hon. Abdulmalik Zubairu ya dauki nauyin aurar da mata marayu 105 a Zamfara. Hoto: Abdulmalik Zubairu Bungudu.
Asali: Facebook

Zamfara: Dan Majalisa ya tallafawa marayu

Kara karanta wannan

Samoa: Tinubu zai dauki mataki kan Daily Trust game da rahoton yarjejeniyar da aka yi

Abdulmalik ya bayyana haka ne bayan daura auren da Sheikh Liman Musa Kura ya jagoranta a garin Bungudu, kamar yadda ya tabbatar a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan Majalisar ya ce ya yi hakan ne domin rage musu dawainiya ganin cewa iyayensu sun rasu.

Ya ce sai da aka kafa kwamitin bincike mai karfi wurin zakulo mata da suka dace a mazabu 21 da ke yankinsa.

Zamfara: Musabbabin daukar nauyin aurar da marayu

Ya ce a Musulunci iyaye ne ke da alhakin daukar nauyin auren ƴaƴansu amma tun da marayu ne ya dauke musu wannan wahalar.

Har ila yau, Abdulmalik ya ce ya sayi gadaje da kujeru da sauran kayayyakin daki ga ma'auratan domin bikin cika shekara daya a Majalisa.

Daga bisani ya tallafawa ma'auratan da N100,000 da kuma N50,000 domin kula da kansu bayan sun yi aure.

Kara karanta wannan

Dambarwar Sultan: Dalilai da ka iya jawo Gwamna Aliyu rasa kujerarsa a 2027

Auren marayu ya jawo kace-nace a Niger

Kun ji cewa Kakakin Majalisar jihar Niger ya dauki nauyin auren mata marayu wanda ya jawo cece-kuce a fadin Najeriya.

Hon. Abdulmalik Sarkin-Daji ya dauki nauyin auren wasu mata marayu 100 inda Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta maka shi a kotu kan haka.

Kennedy-Ohanenye ta ce hakan ya saba ka'ida inda ta bukaci koya musu sana'o'i madadin daura musu aure a wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.