“Ka Hakura da Kuri’un ’Yan Arewa a 2027”: An Ba Tinubu Shawara Kan Samoa

“Ka Hakura da Kuri’un ’Yan Arewa a 2027”: An Ba Tinubu Shawara Kan Samoa

  • An ba Bola Tinubu shawara da ya manta da kuri'un 'yan Arewa a zaben 2027 bayan cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa
  • Jigon PDP, Abdul-aziz Abubakar ya ce 'yan Arewa ba za su zabi Tinubu ba a 2027 inda ya ce a yanzu ya kai su bango
  • Abdul-aziz ya ce babu yadda za a yi Tinubu ya yi nasara da kuri'un Kudu maso Yammacin kasar wato yankin da ya fito

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar PDP a Najeriya, Abdul-aziz Na'ibi Abubakar ya yi tsokaci kan zaben 2027 da 'yan Arewa.

Abdul-aziz ya ce Bola Tinubu ba zai taba samun kuri'un 'yan Arewa ba musamman bayan sanya hannu a yarjejeniyar Samoa.

Kara karanta wannan

Samoa: Gwamnati ta magantu kan ikirarin 'yan Arewa za su guji Tinubu a 2027

An shawarci Tinubu ya manta da kuri'un ƴan Arewa a 2027
Jigon PDP ya ce ƴan Arewa sun gama zaben Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Samoa: Jigon PDP ya shawarci Tinubu

Jigon PDP ya bayyana haka ne a jiya Asabar 6 ga watan Yulin 2024 a shafinsa na X inda ya ce Tinubu ya barar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na'ibi ya ce zai yi wahala yankin Kudu maso Yammacin Najeriya su iya kawo Tinubu a zaben domin ba shi dama ta biyu.

Ya ce Tinubu da ya fadi jiharsa ta asali wato Osun da kuma Lagos babu abin da zai tabuka ba tare da 'yan Arewa ba.

"Zaku yi ta korafi har karshen duniya amma Tinubu ba zai samu kuri'un 'yan Arewa ba a zaben 2027."
"Bari mu gani ko Kudu maso Yammacin kasar za su mayar da shi kujerar shugabanci karo na biyu."
"Mutumin da ya fadi Lagos da asalin jiharsa ta Osun bai kamata yana alfahari da kuri'u ba ko kuma takalar yankin da suka ba shi mafi yawan kuri'u."

Kara karanta wannan

"Za mu gama da su": Sanata ya yi wa Tinubu alkwarin murkushe PDP a zaben da za a yi

- Abdul-aziz Abubakar

Cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa a Najeriya

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Arewa da dama suka fusata kan yarjejeniyar Samoa da ake zargin akwai auren jinsi a ciki.

Sai dai gwamnatin ta yi karin haske inda ta ce ta sanya hannu ne a bangaren tattalin arziki ba auren jinsi ba kamar yadda ake yadawa.

Malaman Musulunci da dama a yankin sun yi Allah wadai da wannan yarjejeniya inda suka nuna bacin ransu a hudubobin Juma'a.

'Yan Arewa na tare da APC - Hadimin Tinubu

Kun ji cewa hadimin Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan zaben 2027 da ake cewa 'yan Arewa za su yaki shugaban.

Dada Olusegun ya ce 'yan Arewa za su sake zaben Tinubu a 2027 kamar yadda suka yi a 2023 duk da nufin wasu mugaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.