Kwana 1 da Zaman Kotu, Gwamna Ododo Ya Dauki Mataki Kan Ciyamomi 21

Kwana 1 da Zaman Kotu, Gwamna Ododo Ya Dauki Mataki Kan Ciyamomi 21

  • Gwamnatin jihar Kogi ta kara wa'adin shugabannin riko na kananan hukumomi 21 da ke jihar da suke shirin sauka
  • Majalisar jihar ita ta amince da tsawaita wa'adin bayan Gwamna Usman Ododo ya rubuta mata takarda kan lamarin
  • Wannan na zuwa ne yayin da shugabannin rikon ke karkare wa'adinsu a ranar 8 ga watan Yulin 2024 kafin karin wa'adin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya tsawaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi a jihar.

Majalisar jihar ta kara wa'adin shugabannin rikon ne zuwa watanni shida domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Gwamna Ododo ya tsawaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi
Gwamna Usman Ododo ya amince da karin wa'adin shugabannin kananan hukumomi 21 a jihar Kogi. Hoto: Ahmed Usman Ododo.
Asali: Facebook

Kogi: Ododo ya kara wa'adin ciyamomi 21

Kara karanta wannan

Dambarwar Sultan: Dalilai da ka iya jawo Gwamna Aliyu rasa kujerarsa a 2027

Wannan mataki na zuwa ne yayin zaman Majalisar a yau Juma'a 5 ga watan Yulin 2024 a birnin Lokoja, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ododo shi ya tura wasikar neman karin wa'adin ga shugabannin riko na kananan hukumomin ga Majalisar.

Ododo a cikin takardar ya bayyana matsalar kudi daga cikin dalilan da zai hana gudanar da zaben kananan hukumomin, Punch ta tattaro.

Kakakin Majalisa ya shawarci ciyamomin jihar Kogi

Kakakin Majalisar, Hon. Umar Yusuf shi ya karanto takardar ga mambobin inda ya hori shugabannin rikon kan aiki.

Hon. Umar ya bukace su da su zama jakadun kananan hukumomin da suke jagoranta a kowane lokaci.

Wa'adin shugabannin rikon kananan hukumomi 21 zai kare ne a ranar 8 ga watan Yulin 2024 na wannan shekara.

Bayan matakin Majalisar na karin wa'adin, shugabannin za su kammala wa'adin nasu a ranar 8 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Aliko Dangote ya bayyana tsawon lokacin da za a dauka wajen farfado da tattalin arziki

Kotu ta yi hukunci kan zaben Kogi

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben jihar Kogi da aka gudanar.

Kotu ta yi fatali da korafin dan takarar jam'iyyar SDP, Muritala Ajaka da ke kalubalantar zaben Usman Ododo na APC.

Wannan na zuwa ne bayan sanar da Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben jihar na watan Nuwambar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.