Abdullahi Ganduje: Kotu ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Shugabancin Jam'iyyar APC

Abdullahi Ganduje: Kotu ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Shugabancin Jam'iyyar APC

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sanya ranar yanke hukuncin kan shari'ar shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje
  • Wasu 'yan jam'iyyar daga Arewa ta Tsakiya ne su ka shigar da kara su na tuhumar sahihancin kasancewar Ganduje a kan kujerar
  • Bayan Mai Shari'a Inyang Ekwo ya kammala sauraron bangarorin biyu, sai ya sanya ranar 18 ga watan Satumba domin yanke hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje zai san matsayarsa kan jagorancin jam'iyyar yayin da kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari'ar.

Wasu 'yan jam'iyyar, karkashin inuwar 'yan APC na Arewa ta Tsakiya ne su ka shigar da kara bisa zargin cewa an kakaba masu Ganduje a matsayin shugaba.

Kara karanta wannan

"Bashi mai sharudan shaidanci": Shehu Sani ya magantu kan yarjejejniyar Samoa

Abdullahi Ganduje
Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin shugabancin APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayyana cewa wannan dambarwa za ta zo karshe ranar 18 Satumba, 2024 da za a yanke hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An saurari lauyoyi a shari'ar Ganduje

A yau Juma'a ne Mai Shari'a Inyang Ekwo ya saurari lauyoyin Abdullahi Umar Ganduje da na 'yan jam'iyyar daga Arewa ta Tsakiya kan kalubalantar yadda ake shugabancin APC.

Wadanda su ka shigar da kara karkashin Saleh Zazzage na kalubalantar kasancewar Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam'iyyar APC bisa rashin cancanta, The Guardian ta wallafa.

Su na rokon kotun ta gaggauta haramtawa Abdullahi Umar Ganduje ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban APC kasancewar lokaci ne na dan jam'iyyar daga Arewa ta Tsakiya ya jagorancesu.

An nemi kotu ta dakatar da Ganduje

A wani labarin kun ji cewa tsohon dan takarar shugabancin jam'iyyar APC, Mohammed Sa'idu Etsu ya nemi kotu ta kori Abdullahi Ganduje daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Matashin da ya hallaka masallata a Kano ya amsa laifinsa, Kotu ta fitar da matsaya

Tsohon dan takarar ya nemi kotu ta kori Ganduje bisa zargin cewa a nada shi ba bisa ka'ida ba, wanda hakan ya saba da kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel