Wike vs Kingibe: Kungiya a Arewa Ta Yi Gargadi Kan Taba Kimar Tinubu, Ta Gano Manaƙisa

Wike vs Kingibe: Kungiya a Arewa Ta Yi Gargadi Kan Taba Kimar Tinubu, Ta Gano Manaƙisa

  • Kungiya a Arewacin Najeriya ta yi magana kan rigimar da ke tsakanin Nyesom Wike da Sanata Ireti Kingibe a Abuja
  • Kungiyar mai suna Arewa Youths for Peaceful Coexistence ta gargaɗi Kingibe da sauran masu sukar Wike kan taba martabar Bola Tinubu
  • Shugaban kungiyar, Haruna Bature shi ya bayyana haka inda ya ce ana ƙoƙarin batawa Tinubu suna a birnin Tarayya Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Arewa Youths for Peaceful Coexistence ta dauki zafi kan rigimar Nyesom Wike da Ireti Kingibe.

Kungiyar ta soki Sanata Kingibe kan sukar Wike da ta ke yi inda ta ce hakan neman bata Shugaba Bola Tinubu ne.

Kara karanta wannan

"Muna tsoron faruwar irin zanga-zangar Kenya": Jigon APC ya gargadi Tinubu

Kungiya ta yi gargadi kan taba kumar Tinubu a rikicin Wike da Kingibe
Kungiyar matasa ta ja kunne kan batawa Tinubu suna a rigimar Wike da Kingibe a Abuja. Hoto: @Iretikingibe, @GovWike.
Asali: Twitter

An yi gargadi kan bata sunan Tinubu

Shugaban kungiyar, Haruna Bature shi ya bayyana haka inda ya gargadi mutane kan sukar Wike da kuma Bola Tinubu, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bature ya bukaci Kingibe da sauran masu aikata hakan da su gane lokacin zabe ya wuce a yanzu mulki ake yi.

"Mun gano wani bidiyo inda Aisha Yesufu ke caccakar Wike kan kalamansa na kin zaben Sanata Ireti Kingibe."
"Muna jan hankalin mutanen Abuja da su sani an fara wannan rigima ne domin sukar kokarin Tinubu ta ofishin Nyesom Wike."
"Wannan kalamai na Kingibe ya na da alaƙa da neman kawo cikas a gwamnatin Tinubu a kokarin da ta yi a cikin shekara daya kacal."

- Haruna Bature

Alakar Nyesom Wike-Kingibe tayi tsami

Wanna na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigima da kuma mayar da martani tsakanin Wike da Kingibe a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya tona 'yan Arewan da ke kokarin ganin bayan Tinubu a zaben 2027

Wike shi ne Ministan Abuja yayin da Sanata Kingibe ke wakiltar al'ummar birnin a Majalisar Dattawa.

A kwanakin baya, Kingibe ta yi zargin an mayar da ita saniyar ware tun daga Majalisar a wasu kwamitoci da ke da alaka da kasafin kudin Abuja.

Wike ya yi barazana ga Sanata Kingibe

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi barazana ga Sanata Ireti Kingibe kan kayar da ita zaben 2027 a Abuja.

Wike ya ce Kingibe za ta gane shafi ruwa ne a zaben 2027 saboda babu wani dan Abuja da zai zabe ta kuma sai ya ga bayanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.