Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Tsige 'Yan Majalisa 25 da Suka Bar PDP Zuwa APC

Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Tsige 'Yan Majalisa 25 da Suka Bar PDP Zuwa APC

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta soke umarnin hana ƴan majalisa 25 na jihar Rivers da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC ayyana kansu a matsayin ƴan majalisa
  • Kotun mai alƙalai uku da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta ce babbar kotun jihar Rivers ba ta da hurumin sauraron ƙarar
  • Mai shari'a Jimi Bada ya yi hukunci cewa kotun ta tauye haƙƙin ƴan majalisar saboda ba ta ji daga garesu ba kafin ba da umarnin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara ta soke umarnin da babbar kotun jihar Rivers ta yi na hana mambobi 25 na majalisar dokokin jihar ayyana kansu a matsayin ƴan majalisa ko yin ayyukan majalisa.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Kotu ta ba lauyoyi sabon umarni a shari'ar masarautun Kano

Ƴan majalisar waɗanda ke yin biyayya ga ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike sun sauya sheƙa ne daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Kotu ta yi hukunci kan rikicin majalisar dokokin Rivers
Kotun daukaka kara ta soke hukuncin hana 'yan majalisa 25 na Rivers ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa Hoto: @DeeOneAyekotoo, @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Rikicin Rivers: Wane hukunci kotu ta yi?

A hukuncin da kotun mai alƙalai uku ta yanke a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli, ta ce babbar kotun jihar Rivers ba ta da hurumin sauraron ƙarar, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shigar da ƙarar ne dai kan ko kujerun ƴan majalisar waɗanda suka sauya sheƙa sun zama babu kowa a kansu ko wa'adinsu na ofis ya ƙare.

Meyasa kotu ta yanke hukuncin?

Kotun ta bayyana cewa sashe na 273(3) na kundin tsarin mulki ya ce babbar kotun tarayya ce kaɗai ke da hurumin yanke cewa kujerar ɗan majalisa babu kowa a kanta ko wa'adinsa na ofis ya ƙare, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 4 a wani hari a jihar Katsina

Da yake yanke hukunci, mai shari'a Jimi Bada ya bayyana cewa kotun ta tauye haƙƙin ƴan majalisun ta hanyar ƙin ji daga garesu kafin ta bayar da umarnin hana su ayyana kansu a matsayin ƴan majalisa.

Mai shari'a Jimi Bada ya nuna cewa babu wata gaggawa da za ta sanya babbar kotun ta jihar Rivers ta bayar da umarnin

Sauran alƙalan kotun ɗaukaka ƙarar, mai shari'a Hamma Barka da mai shari'a Bilkisu Aliyu sun amince da hukuncin.

Kotun ɗaukaka ƙara ta tanadi hukunci

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta shirya yanke hukunci a shari'ar tsige Martin Amaewhule da sauran ƴan majalisar dokokin jihar Ribas 24.

Ana fafata shari'ar ne tsakanin ƴan majalisa 25 ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Martin Amaewhule da kuma ƴan majalisar da ke ƙarƙashin jagorancin Victor Oko Jumbo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel