Zaben Edo: PDP Ta Yi Watsi da Hukuncin Kotu, Ta Dage Cewa Ighodalo ne Dan Takararta
- Jam'iyyar PDP ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan zabenta na fidda dan kujerar gwamnan jihar Edo
- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke zaben PDP na watan Fabrairun 2024 saboda an cire sunayen wasu wakilai 378 ba bisa ka'ida ba
- Jam'iyyar PDP ta dage kan cewa Asue Ighodalo shi ne zai ci gaba da kasancewa dan takararta na gwamnan Edo duk da hukuncin kotun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Edo - A ranar Alhamis ne PDP ta yi martani kan hukuncin kotu na soke zaben fidda gwanin da ta yi na gwamnan jihar Edo, inda ta dage cewa Asue Ighodalo ne dan takararta.
Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya soke zaben fidda gwamin PDP na Fabrairun 2024 bisa hujjar cewa an cire sunayen wasu wakilai 378 ba bisa ka'ida ba.
PDP ta dage Ighodalo dan takararta
Sai dai jam’iyyar ta dage cewa Asue Ighodalo shi ne zai ci gaba da kasancewa dan takararta a zaben gwamnan Edo da za a yi a ranar 21 ga Satumba, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jim kadan bayan hukuncin kotun, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Edo, Dr Tony Aziegbemi ne ya fitar da sanarwa cewa:
Sanarwar PDP kan takarar gwamnan Edo
“Bari mu jaddada maku cewa har yanzu Dakta Asue Ighodalo shi ne mai rike da tutar takarar kujerar gwamnan Edo a jam’iyyarmu a zaben 2024.
Kuma mu na so ku sani cewa, hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke bai shafi takarar Dakta Asue Ighodalo ko kadan ba.”
Edo 2024: Jita-jita kan takarar Ighodalo
Jam’iyyar ta yi zargin cewa akwai wasu bata gari da ke yada jita-jita game da dan takararta, inda ta ce suna tsoron farin jinin Ighodalo ne kawai.
Duk da dai ba ta bayyana sunayen wadanda ke yada jita-jitar ba, amma dai PDP ta yi kira ga mambobinta da su kwantar da hankalinsu, tare da cewa babu abin da zai sauya.
“Jam’iyyar PDP tana sane da cewa wasu bata gari da ke fargabar farin jinin dan takararmu Dakta Asue Ighodalo suna ta yada jita-jitar cewa an soke takarar shi."
- Shugaban jam'iyyar PDP.
Ba a san makomar PDP a zaben Edo ba
Yanzu da kotu ta soke zaben fidda gwani na gwamna na PDP, makomar jam’iyyar a zaben jihar Edo na tangal-tangal, komai na iya faruwa.
Sai dai ba a bayyana ko jam’iyyar za ta daukaka kara domin rusa hukuncin umurnin babbar kotun tarayya da ke Abuja ba.
Kotu ta rusa zaben PDP na Edo
Tun da fari, mun ruwaito cewa babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Edo.
Mai Shari'a, Inyang Ekwo wanda ya yanke wannan hukunci ya ce akwai wasu wakilai 378 da ya kamata su kada kuri'a a zaben amma jam'iyyar ta cire su ba bisa ka'ida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng