An Jikawa PDP Aiki, Kotu Ta Yi Hukunci Kan Zaben Fitar da Gwani Ana Daf da Zabe

An Jikawa PDP Aiki, Kotu Ta Yi Hukunci Kan Zaben Fitar da Gwani Ana Daf da Zabe

  • Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Edo
  • Kotun ta ce an saba dokokin kasa wurin gudanar da zaben wanda aka yi a watan Faburairun 2024 a jihar
  • Zaben da aka gudanar na PDP shi ya ba Asue Ighodalo nasarar zama sahihin dan takarar jam'iyyar a zaben da za a yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan sahihancin zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Kotun ta rusa zaben da aka gudanar a watan Faburairun 2024 wanda ya ba Asue Ighodalo nasarar zama dan takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hango matsala, Sanatoci sun koka kan shigo da gurbataccen mai a Najeriya

Kotu ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP ana daf da zabe
Babbar Kotun Tarayya ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Edo. Hoto: Asue Ighodalo.
Asali: Facebook

PDP: Hukuncin kotun kan zaɓen Edo

Channels TV ta tattaro cewa Mai Shari'a, Inyang Ekwo ya yanke wannan hukunci inda ya ce ba a bi ka'idojin gudanar da zaben ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ekwo ya ce kwata-kwata ba a bi tsarin doka ba inda aka cire daliget 378 ba bisa ka'ida ba wurin gudanar da zaben fidda gwanin, cewar AIT News.

Alkalin kotun ya ce an saba dokokin zabe da kuma tsare-tsaren jam'iyyar PDP yayin da ake gudanar da zaben fidda gwanin a filin wasa na Samuel Ogbemudia a Benin.

Edo: Wadanda suka shigar da korafi

Kevin Mohammed shi ya shigar da korafin a madadin sauran daliget da abin ya faru da su a zaben domin kalubalnatar hakan.

Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben a watan Satumbar 2024 da mu ke ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Manyan dalilai 3 da za su iya jawo Buhari ya goyi bayan takarar Atiku a zaben 2027

Jigon PDP ya yi murabus a Edo

A wani labarin, kun ji cewa 'dan kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Edo, Prince Felix Isuku, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Babban jigon ya fice daga jam'iyyar PDP yayin da harkokin kamfe suka kankama ana daf da zaɓen gwamnan Edo wanda za a yi a watan Satumba 2024.

Prince Isuku ya bar PDP ne sa'o'i 48 bayan kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ta jihar Edo ya kori tsohon mataimakin gwamna, Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel