'Ba Kamar Yadda Ake Zato Ba', Yakubu Dogara Ya Fadi Yawan Albashinsa a Majalisa

'Ba Kamar Yadda Ake Zato Ba', Yakubu Dogara Ya Fadi Yawan Albashinsa a Majalisa

  • Tsohon kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Hon. Yakubu Dogara ya fayyace komai kan kuɗin da mambobin suke samu
  • Dogara ya ce bayyana gaskiya kan yawan kudi da suke samu ya zama dole saboda yadda ake zargin suna samun makudan kuɗi
  • Ya ce lokacin da ya ke shugabancin Majalisar albashinsa N400,000 ne da kuma alawus na N25m kacal ba kamar yadda ake zato ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon kakakin Majalisar Tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya fadi yawan alawus da ake ba shi.

Yakubu Dogara ya ce kwata-kwata albashinsa bai wuce N400,000 ba a lokacin da ya shugaban Majalisar.

Dogara ya fadi yawan albashin da ya ke samu lokacin shugabancin Majalisar
Yakubu Dogara ya ce N400,000 ne kadai albashinsa lokacin da ya ke shugabantar Majalisar. Hoto: Hon. Yakubu Dogara.
Asali: Facebook

Dogara ya fadi yawan albashinsa a Majalisa

Kara karanta wannan

"A koma salon mulkinsu Sardauna": An fadawa Tinubu hanyar magance matsalolin Najeriya

Tsohon kakakin Majalisar ya kuma bayyana cewa ana ba shi alawus na N25m ne a lokacin, Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce fayyace hakan ya zama dole ganin yadda mutane suke zaton makudan kudi ƴan Majalisar ke samu a banza, cewar Channels TV.

"Lokacin da na ke kakakin Majalisar Tarayya, ana ba ni albashin N400,000 a wata da kuma alawus na N25m."
"Na umarci mai kula da kudi na ya bude wani asusun daban domin zuba kudin alawus saboda na al'umma ne wannan."
"Ya yi mun korafi cewa mutane suna yawan roko sai na ce masa idan kudin suka kare ya ci bashi, idan wasu sun shigo sai ka maye gurbinsu da shi."

- Yakubu Dogara

Rt. Hon. Dogara ya ba ƴan Najeriya shawara

Dogara ya shawarci ƴan Najeriya da su bar wakilansu su yi musu aiki madadin yawan tambayansu kudi.

Kara karanta wannan

"Kar a bari rashin tsaro ya kara kamari a Arewa," Atiku Abubakar

Ya ce duk abin da ake fada kan yawan kudi da suke samu kwata-kwata ba haka ba ne kawai zargi ne maras tushe.

Dogara ya caccaki Nyesom Wike

A baya, kun ji cewa tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara ya maidawa Nyesom Wike martani kan rikicin da suke yi.

A wasu maganganu da ya yi a shafinsa na Twitter, Dogara ya yi raddi ga Gwamna Nyesom Wike wanda ya zarge shi da rashin dattaku.

Wike ya soki Yakubu Dogara bisa zargin cewa ya gagara cika alkawarin da ya dauka, saboda yana goyon bayan Atiku Abubakar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.