An Fasa Kwai: Yadda Aka Raba Cin Hanci Domin Obasanjo Ya Shekara 12 a Ofis

An Fasa Kwai: Yadda Aka Raba Cin Hanci Domin Obasanjo Ya Shekara 12 a Ofis

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara ya bayyana yadda aka so rufe bakinsa domin tazarcen Olusegun Obasanjo a 2006
  • Adolphus Wabara ya bayyana cewa an kawo masa makudan kudi domin ya tabbatar da kudirin da zai ba Obasanjo wucewa karo na uku
  • Har ila yau, tsohon shugaban majalisar ya bayyana dalilan da suka hana shi yarda da kudirin duk da makudan kudin da aka tura masa har gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Adolphus Wabara ya yi karin haske kan neman tazarcen Olusegun Obasanjo a 2006.

Sanata Adolphus Wabara ya ce akwai wasu Sanatoci da suka goyi bayan tazarcen kuma sune suka rika ruruta maganar a majalisa.

Kara karanta wannan

"A koma salon mulkinsu Sardauna": An fadawa Tinubu hanyar magance matsalolin Najeriya

Wabara
Wabara ya fadi yadda aka so ba shi cin hanci domin tazarcen Obasanjo. Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanatan Wabara ya bayyana makudan kudin da aka tura masa gida a lokacin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wabara ya ki yarda da tazarcen Obasanjo

Sanata Adolphus Wabara ya bayyana cewa mutanensa ba su goyi bayan mulkin Obasanjo karo na uku ba kuma saboda haka ne bai goyi bayan kudirin ba.

Tsohon shugaban majalisar ya bayyana cewa ilimi mai inganci da wayewa da ya samu ne suka tallafa masa wajen yaki da kudirin tazarcen Olusegun Obasanjo.

An ba Sanata Wabara cin hanci kan tazarce

Adolphus Wabara ya bayyana cewa a lokacin an ba shi kudi har N250m domin ya amince da tazarcen Obasanjo.

Ya kara da cewa an kawo masa kudin ne har gida da misalin karfe 1:30 na safe a cikin wata mota amma ya ki karba, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin manyan mukamai 8 a Gwamnatin tarayya

Yanayin da Najeriya ke ciki a yau

Sanata Adolphus Wabara ya koka kan yadda shugabanni suka bar talauci ya yi katutu ga al'ummar Najeriya.

Wabara ya zargi yan siyasa da kirkiro yunwa da gangan domin sanya talakawa su rika binsu suna ba su abinci.

PDP ta ba Wabara babban mukami

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta tabbatar da Sanata Adolphus Wabara a matsayin shugaban kwamitin amintattu (BoT) na ƙasa.

A taron BoT karo na 76 da aka yi da ya wuce, an kuma naɗa tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Maƙarfi, a matsayin sakataren kwamitin na BOT.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng