Hukuma Ta Sanya Ranar Zaben Kananan Hukumomi Ana Cikin Takaddama a Rivers

Hukuma Ta Sanya Ranar Zaben Kananan Hukumomi Ana Cikin Takaddama a Rivers

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Rivers (RSIEC) ta shirya gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar
  • Hukumar ta sanya ranar, 5 ga watan Oktoban 2024 domin gudanar da zaɓen bayan gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya rantsar da shugabannin riƙon ƙwarya
  • Sanya lokacin gudanar da zaɓen na zuwa ne yayin da ake jiran hukuncin kotu kan taƙaddamar da ake yi dangane da shugabancin ƙananan hukumomin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta sanya ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.

Hukumar zaɓen ta sanar da ranar 5 ga watan Oktoban 2024 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

An cafke wasu daga cikin masu hannu a harin bam a Borno

An sanya ranar zaben kananan hukumomi a Rivers
Za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Rivers a watan Oktoba Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Sanarwar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan kujerar shugabancin ƙananan hukumomi a jihar, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana taƙaddama kan kujerar ciyamomi a Rivers

Taƙaddamar dai ta faru ne sakamakon rikicin da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Gwamnan ya ƙaddamar da shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomin yayin da tsofaffin ciyamomin suka tubure cewa har yanzu suna kan mulki bayan ƙara musu wa'adin watanni shida da ƴan majalisar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule suka yi.

A kwanakin baya an gudanar da zanga-zanga tare da hana tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin shiga ofis bayan wa'adin mulkinsu ya ƙare.

Domin kaucewa ɓarkewar rikici, ƴan sanda sun kulle dukkanin sakatariyoyin ƙananan hukumomin jihar guda 23 har zuwa lokacin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yi hukunci kan ƙarar da aka shigar a gabanta.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun kwararo zuwa jihar Neja daga kasashen waje? An gano gaskiya

Gwamna Fubara ya ba shugabannin riƙo dama

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya ce shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi 23 za su iya gudanar da ayyukansu daga ko’ina.

Gwamna Fubara ya yanke wannan shawarar ne bayan da ƴan sanda suka kulle sakatariyoyin ƙananan hukumomin tare da jibge jami'an tsaro a ranar Talata, 18 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng