Kano: Har Yanzu Ganduje Bai Tsira Ba, Abba Ya Taso Shi Gaba a Wata Sabuwar Badakala

Kano: Har Yanzu Ganduje Bai Tsira Ba, Abba Ya Taso Shi Gaba a Wata Sabuwar Badakala

  • Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin bincikar tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje
  • Abba ya bayyana haka yayin kaddamar da sake biyan kudin giratuti ga tsofaffin ma'aikata a jihar da suka bar aiki
  • Gwamnan ya zargi gwamnatin da ta shude da zaftare makudan kudi na giratuti inda kuma ba a mayar da su asusun gwamnati ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda aka tafiyar da biyan giratuti a baya.

Gwamnan ya sha alwashin bankado badakalar da aka yi a lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Abba Kabir zai sake kaddamar da bincike kan gwamnatin Ganduje
Gwamna Abba Kabir ya zargi Abdullahi Ganduje da badakalar kudin giratuti a jihar Kano. Hoto: @Kyusufabba, Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: Twitter

Kano: Abba Kabir zai binciki badakalar Ganduje

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta da shari’ar zabe ba su taka masa burki ba, an nada Abba gwarzon Gwamnoni

Abba ya zargi Ganduje da zaftare wasu kudade na giratuti a jihar ba tare da mayar da su asusun gwamnati ba, kamar yadda Channels TV ta wallafa faifan bidiyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya koka kan yadda babu wani shaida da zai tabbatar da ƴan fansho na bin gwamnatin bashi saboda rashin shaida da takardu na kuɗin da aka zaftare.

"Mun rasa ya za mu yi, ba za mu iya gano kudin fansho da gwamnatin da ta shude da cire ba a jihar."
"Mun yi dukkan kokari domin gano kudin inda muka tabbatar an cire su amma babu duriyarsu, ku yi duk mai yiwuwa domin nemo inda kudinku suka shiga."

- Abba Kabir

Abba ya ba kungiyar ƴan fansho shawara

Gwamna Abba daga bisani ya shawarci kungiyar ƴan fansho da ta rubuta korafi ga gwamnatin jihar domin neman inda kudin suke.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta dauki mataki bayan Tinubu ya yi biris da maganar ƙarin albashi

Abba ya ce gwamnatin jihar za ta yi iya bakin kokarinta wurin binciko inda kuɗin suka maƙale tare da biyansu hakkinsu.

Abba ya kaddamar da biyan giratuti

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da kashi na biyu na biyan kuɗin giratuti N5bn daga shekarar 2016 zuwa 2019.

A kashi na farko, Gwamnan ya fitar da N6bn domin biyan kuɗin giratuti da waɗanda suka rasu mutum 5,333 wanda ya sanya suka kai N11bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel