“Ku Yi Masa Adalci”; Shettima Ya Roki ’Yan Najeriya Alfarma 1 Game da Tinubu
- Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya tura roko ga 'yan Najeriya kan mulkin Shugaba Bola Tinubu
- Shettima ya bukaci 'yan kasar su yi adalci wurin kimanta mulkin Bola Tinubu yayin da yake kokarin inganta kasar
- Tsohon gwamnan Borno ya tabbatar da himmatuwar gwamnatin Tinubu wurin inganta tattalin arziki da dakile sauran matsaloli
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya roki 'yan Najeriya wurin kimanta gwamnatin Bola Tinubu a kasar.
Shettima ya bukaci 'yan kasar su yiwa Tinubu adalci yayin kimanta gwamnatinsa duba da kokarin da yake yi wurin daidaita kasar.
Kashim ya fadi yadda Tinubu yake aiki
Sanata Shettima ya bayyana haka ne a yau Juma'a 28 ga watan Yunin 2024 yayin wani babban taro a Abuja, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Borno ya ce Tinubu na aiki ba dare ba rana domin ganin ya inganta Najeriya baki daya.
Ya kuma ba da tabbacin cewa Tinubu yana iya bakin kokarinsa wurin tabbatar da komai ya daidaita a kasar, kamar yadda VON ta tattaro.
Kashim ya magantu kan matsalar tattalin arziki
Ya ce matsalar tattalin arziki ba iya Najeriya ba ne kadai inda ya ce duk duniya ana fama da wannan matsalar.
Har ila yau, Shettima ya ce bai taba ganin lokacin da Najeriya ta samu shugaba mafi kwarewa mai kishin kasa irin yanzu ba.
Shettima ya roki 'yan Najeriya da su ba shi dukkan gudunmawa da goyon baya domin samun abin da ake nema.
Har ila yau, ya bayyana irin shirin da Tinubu ke yiwa kasar a matsayinsa na kwararren shugaba mai hazaka da hangen nesa.
Tinubu ya koka kan matsalolin Arewa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya nuna damuwa kan yadda matsalolin tsaro ke kara kamari a Arewa.
Tinubu ya ce babban matsalar da ake fama da shi a yankin shi ne rashin shugabanci mai inganci da kuma adalci.
Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashin Shettima ya ce yana iya bakin kokarinsa wurin ingata yankin.
Asali: Legit.ng