"Suna Neman Kassara Tinubu", Kungiyar Arewa Ta Soki Atiku da El Rufai Kan Ziyartar Buhari

"Suna Neman Kassara Tinubu", Kungiyar Arewa Ta Soki Atiku da El Rufai Kan Ziyartar Buhari

  • Kungiyar Arewa Think Tank ta caccaki Nasir El-Rufai da Atiku Abubakar kan ziyarar da suka kai wa Muhammadu Buhari
  • Think Tank ta ce duk munafurci ne kai wannan ziyara saboda neman tuge Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa
  • Ta gargadi masu shirin durkusar da Tinubu da su yi a hankali saboda sai ya karisa wa'adinsa na shekaru takwas kan mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Kungiyar Arewa Think Tank ta caccaki ƴan siyasa da ke ziyartar Muhammadu Buhari a jihar Katsina.

Kungiyar ta ce ba ta ki ƴan siyasa su kai wa junansu ziyara ba amma wannan cike yake da munafurci da kuma cin amana.

Kara karanta wannan

Bukatar Bola Tinubu ta jawo zazzafar muhawara a Majalisar Tarayya, hayaniya ta ɓarke

Kungiyar Arewa ta soki Atiku da El-Rufai kan ziyartar Buhari
Kungiyar Arewa Think Tank ta caccaki El-Rufai da Atiku kan shirinsu na 2027 kan Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Muhammadu Buhari, Atiku Abubakar.
Asali: Twitter

Buhari: Ƙungiya ta soki El-Rufai, Atiku

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Kwamred Mohammed Aliyu Yakubu ya fitar a cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta gargadi masu ziyarar domin neman shawara kan zaben 2027 da su yi hakuri babu wuri a fadar shugaban ƙasa.

Atiku zai hana shugaba Tinubu tazarce?

Think Tank ta bayyana cewa babu wanda zai samu wuri har sai Shugaba Bola Tinubu ya kammala wa'adinsa na shekaru takwas a kan mulki.

Wanna martani na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ziyarci Buhari a Daura.

Daga bisani, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai shi ma ya kai ziyarar wanda jama'a da dama ke hasashen duk a kan zaben 2027 ne.

Kungiya ta gargadi El-Rufai, Atiku kan 2027

"Ziyarar da wasu manyan ƴan siyasar Arewa suka kai wa Buhari duk a kan zaben 2027 domin yiwa Tinubu illa."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu zai gana da gwamnoni, za su tattauna kan mafi ƙarancin albashi a Aso Villa

"Mun gano dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai sun kai masa ziyara a Daura."
"Ziyarar sallah aka kai a bayyane amma akwai makarkashiyar siyasa kan irin wannan yanayi ganin 2027 na tafe."
"Bai kamata tun yanzu masu kwadayin mulki daga Arewa su fara irin wannan shiri ba ganin cewa Tinubu shekara daya kawai ya yi a kan mulki."

- Arewa Think Tank

Atiku ya ziyarci Buhari a gidansa

A wani labarin, kin ji cewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari gidansa da ke Daura.

Atiku ya kai ziyarar domin mika gaisuwar sallah ga tsohon shugaban kasar kammala wa'adinsa na shugabancin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel