Ganduje Ya Ga Ta Kansa, Wasu Manyan Jiga Jigai da Mambobin APC Sun Koma PDP
- Yayin da ake shirin zaben gwamna a jihar Ondo, wasu jiga-jigai da mambobin APC sama da 1000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa PDP
- Masu sauya shekar sun bayyana cewa sun baro APC ne saboda rigingimun cikin gida da kuma kudirinsu na kawar da jam'iyyar da ta kawo 'yunwa'
- Sun kuma sha alwashin cewa za su marawa ɗan takarar gwamna a inuwar PDP baya a zaɓen da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - 'Ya 'yan jam'iyyar APC mai mulki fiye da 1000 a ƙaramar hukumar Akure ta Kudu sun sauya sheƙa zuwa PDP jihar Ondo.
Masu sauya sheƙar karkashin jagorancin Mayowa Ajemoju Boboye sun bayyana rashin bai wa kowa haƙƙinsa a matsayin dalilin barin APC mai mulki.
An fice daga jam'iyyar APC
Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai shugaban jam’iyyar APC na gunduma ta 8, Deborah Owosusi da Ademola Ayonijebul, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran jiga-jigan da ke cikin tawagar masu sauya shekar sun haɗa da Mayowa Boboye, Oloro Alejo, da Azeez Ibrahim wanda ya jagoranci tawagar ƴan Ebira.
Ondo: An sha alwashin karya APC
Sun yi alkawarin goyon bayan PDP da dan takararta na gwamna Hon Agboola Ajayi a zaben gwamnan da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.
A cewarsu za su yi duk mai yiwuwa wajen kawar da jam’iyya mai mulki daga gidan gwamnatin Ondo a zaɓe mai zuwa.
Yadda PDP ta yi masu maraba
Jam'iyyar PDP ta tarbi tsofaffin 'ya 'yan na jam’iyyar APC ne a wani taro da ta shirya ma musamman a babban dakin taro da ke birnin Akure, Vanguard ta ruwaito.
Da yake magana a madadin wadanda suka sauya sheka, tsohon sakataren APC a Akure ta Kudu, Akinwande Fayinminu, ya soki shugabannin APC, inda ya zarge su da kawo yunwa a ƙasa.
"APC ta rasa zaman lafiya da adalci a cikin gida shiyasa kuka ga kawunansu sun rabu, ba za mu iya zama a ciki ba," in ji shi.
Fubara ya zargi mutanen Wike da ta'adi
A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya zargi mutanen Nyesom Wike da hannu a kokarin tashin bam a birnin Fatakwal.
Fubara ya bayyana cewa an shirya tayar da bam ne domin a jawo hankalin gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta ɓaci a Ribas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng