“Siddabarun Siyasa Ne”: Na Hannun Daman Atiku Ya Fadi Dalilin Ziyartar Buhari
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Katsina
- Atiku ya kai ziyarar ne domin gaisuwar salla ga tsohon shugaban kasa a gidansa da ke Daura a jiya Asabar 22 ga watan Yunin 2024
- Masu fashin baki da dama sun yi ta magana kan dalilin ziyarar, sai dai na hannun daman Atiku ya ce duk maganar zaben 2027 ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Na hannun daman Atiku Abubakar ta bayyana dalilin ziyarar dan takarar ga Muhammadu Buhari a Katsina.
Dan jam'iyyar PDP ya ce ganawar ba ta rasa nasaba da shirye-shiryen zaben 2027 da ake tunkara a nan gaba kadan.
Atiku ya ziyarci Buhari a Katsina
Majiyar da ta bukaci boye sunanta ta bayyanawa Daily Trust cewa tattaunawar ta kuma kunshi halin da kasar ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, duk da sun samu sabani a wasu bangarori amma sun tattauna sosai kan zaben da ake tunkara a 2027, Legit ta tattaro.
"Abin da zan iya fada shi ne akwai hikima a ziyarar, ba zan baku cikakkaen bayani ba, amma sun tattauna halin da kasa rke ciki."
"Daga cikin tattaunawar akwai zaben 2023 da kuma zaben 2027 da ake tunkara, ba wai sun tsayar da matsaya ba ne saboda ka san ba wai suna kusanci ba ne."
- Cewar majiyar
Atiku ya magantu kan rikicin PDP
Har ila yau, a ranar Asabar, 22 ga watan Yunin 2024 dan takarar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa dangane da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP.
Atiku ya kuma ziyarci Gwamna Dikko Umaru Radda yayin bayan ziyarartar Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a Nijar.
Atiku ya ziyarci Buhar a Katsina
A wani labarin, kun ji cewa Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci Muhammadu Buhari.
Atiku ya kai ziyarar domin gaisuwar sallah ga tsohon shugaban kasar da suka fafata a zaben 2019 da kuma 2023.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
Asali: Legit.ng