Zaben 2027: Atiku Ya Bayyana Mafita 1 Game da Rikicin da Ya Mamaye PDP a Katsina

Zaben 2027: Atiku Ya Bayyana Mafita 1 Game da Rikicin da Ya Mamaye PDP a Katsina

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana matsayar sa dangane da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar sa ta PDP
  • A ranar Asabar ne dan takarar shugaban kasa a 2023 ya dura jihar Katsina inda ya ziyarci wasu manyan mutane ciki har da Buhari
  • A ziyarar tasa, Atiku ya ƙauracewa magana kan rikicin PDP a jihar amma ya bayyana yadda za a shawo kan lamarin gabanin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Katsina - A ranar Asabar, 22 ga watan Yuni, dan takarar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ƙauracewa magana kan rikicin PDP da ya mamaye jihar Katsina.

Legit Hausa ta ruwaito Atiku ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan sa na Daura a ranar Asabar din domin yi masa gaisuwar babbar Sallah.

Kara karanta wannan

Gaisuwar Sallah ko shirin zaben 2027? Shugabannin Najeriya 3 da Atiku ya ziyarta

Atiku yayi magana akan rikicin PDP bayan ya ziyarci Buhari
Atiku Abubakar ya ba da shawarar shawo kan rikicin PDP a Katsina. Hoto: @Atiku
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya kuma gana da Dr Dikko Umar Radda, gwamnan jihar Katsina, kuma jigo a jam'iyyar APC, a fadar Sarkin Daura, a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mun ruwaito cewa ziyarar da Atiku ya kai a ranar Asabar, ta kara haifar da cece-kuce game da burinsa na siyasa gabanin zaben 2027.

Rikicin PDP: Atiku ya bayyana mafita

Yayin da yake jawabi bayan ganawarsa da Buhari, Atiku ya ce taron jam’iyyar da ke tafe zai warware rikicin da ya dabaibaye PDP a jihar Katsina, inji rahoton Daily Trust.

"Ba da jimawa ba za a yi babban taron jam'iyyar, don haka, mutane za su zabi wanda suke so ya zama shugaban jam'iyyarsu," in ji Atiku.

Abin da ya jawo rikicin PDP a Katsina

Jam'iyyar PDP dai ta kasance cikin rikici tun gabanin zaben 2023 da kuma bayansa, abin da ya jawo tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shehu Shema ya koma APC.

Kara karanta wannan

Ana dambarwar masarauta, Abba ya jajubo ayyuka 25, katangar Sarki za ta ci N99m

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, kungiyar 'manyan masu ruwa da tsaki na PDP' da kwamitin riko na PDP a Katsina sun fara takun saka mai zafi kan batun sayar da fom.

Yayin da kungiyar ke zargin kwamitin ya hana su sayen fom din takara, shi kuma kwamitin ya yi gum da bakinsa kan lamarin duk da tarin kokari na jin ta bakin su kan wannan zargi.

Atiku ya ziyarci IBB, Abdulsalami Abubakar

A wani labarin kuma, Atiku Abubakar ya ziyarci tsofaffin shugabannin kasa, Janar Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar, a Minna, jihar Neja, inda ya kai gaisuwar Sallah.

Ziyarar dai ta janyo martani daga ‘yan Najeriya, inda wasu ke ganin wani yunkuri ne na Atiku na kulla kawance domin tunkarar zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.