Kano: Ana Tsaka da Rigimar Sarauta, Abba Ya Taso Ganduje a Gaba Kan Fadan Daba
- Gwamna Abba Kabir ya nuna damuwa kan yadda fadace-fadacen ƴan daba ke kara ƙamari a Kano duk da matakai da yake dauka
- Gwamnan ya ce yana zargin gwamnatin da ta shude da daukar nauyin ƴan daban domin kawo rudani a jihar
- Abba ya nuna damuwa kan yadda wasu ke zuwa ofishin ƴan sanda domin belin wadanda aka kama da laifin dabanci a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya magantu kan wadanda ke daukar nauyin ƴan daba a jihar.
Gwamnan ya zargi gwamnatin da ta shude da ɗaukar nauyin 'yan daba a Kano da sauran matsaloli tsaro.
Kano: Abba ya zargi Ganduje kan daba
Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin jawabi a gabanin taron Majalisar zartarwar jihar, cewar BBC Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da taron ne a yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024 a birnin Kano yayin da ake tsaka da rikicin sarautar jihar..
''Kowa ya sani kafin mu shigo gwamnati, tsohuwa gwamnati ce ke ɗaukar nauyin 'yan daba, ita ce ke sa su suna yin abin da duk suka ga dama suna cutar da al'umma".
- Abba Kabir
Gwamnan ya nuna damuwa kan yadda tsaro ke kara tabarbarewa a jihar musamman harkar dabanci.
Sai dai kuma gwamnan ya zargi wasu mutane da daukar nauyin ƴan daba daga jihohi makwabta domin hargitsa jihar Kano.
Abba zai tona asirin waɗanda yake zargi
Ya yi barazanar fara kiran sunayen wadanda ya ke zargi da daukar nauyin ƴan daba a jihar baki daya.
Wannan na zuwa ne yayin da ake yawan samun fadace-fadace na ƴan daba a birnin Kano a ƴan kwanakin nan.
Ƴan daba sun jikkata jami'an tsaro 2
A wani labarin, kun ji cewa wasu miyagu sun yi ajalin wani mutum a jihar Kano tare da jikkata jami'an ƴan sanda biyu.
Lamarin ya faru ne a Unguwar Jaen Makera inda ake yawan samun matsaloli na fadace-fadace na yan daba.
Kwamishinan yan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel shi ya tabbatar da haka inda ya ce sun dauki mataki.
Asali: Legit.ng