Sanusi II vs Aminu: Hadimin Gwamna da Fitaccen Lauya Sun Samu Saɓani Kan Hukuncin Kotu

Sanusi II vs Aminu: Hadimin Gwamna da Fitaccen Lauya Sun Samu Saɓani Kan Hukuncin Kotu

  • Hukuncin babbar kotun tarayya a shari'ar sarautar Kano ya haddasa saɓani tsakanin hadimin gwamna da Abba Hikima
  • Mai magana da yawun Abba Kabir ya ce hukuncin ya rusa masarautu biyar yayin da Hikima ke ganin har yanzu Aminu Bayero ne Sarkin Kano
  • Tun farko kotun ta soke duk wani mataki da Gwamnatin Abba ta ɗauka na fara aiki da sabuwar dokar masarautar Kano ta 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukuncin da babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta yanke a shari'ar sarauta ya kawo ruɗani da saɓanin fahimta.

Sakataren yaɗa labaran Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature da fitaccen lauyan nan, Abba Hikima sun samu saɓani kan ma'anar hukuncin kotun.

Kara karanta wannan

"Ba a sauke Sanusi II ba," Gwamnatin Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncun kotu

Sanusi da Aminu Ado Bayero.
Kakakin Gwamna Abba da lauya sun yi saɓani a hakuncin kotu kan shari'ar sarauta Hoto: Imran Muhammad, Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Facebook

Mutanen biyu sun yi ja-in-ja game da abin da allkalin kotun ke nufi da hukuncin a lokacin da suka haɗu a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kano ta tabbatar da sauke Aminu

A mahangarsa, kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature ya ce hukuncin kotun ya ƙara tabbatar da rusa masarautu biyar da Abdullahi Ganduje ya kirkiro a 2019.

"Ya kamata mutane su gane cewa hukuncin jiya mu ya ɗora a sama saboda dalilai masu yawa. Na farko alkali ya yarda da sabuwar dokar masarauta ta 2024 wacce ta rusa masarautu biyar.
"Saboda haka hukuncin ya tabbatar da tuɓe Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu daga sarauta har sai kotun ɗaukaka ƙara ta yi hukunci."

- Sanusi Bature.

Abba Hikima ya faɗi sahihin Sarkin Kano

Da yake mayar da martani ga kalaman Bature, Abba Hikima ya ce hukuncin kotun ya fito fili, babu wani ruɗani a cikinsa.

Kara karanta wannan

Lauya ya ci gyaran gwamna, ya fassara hukuncin Alkali a shari’ar masarautar Kano

Lauyan ya bayyana cewa mataki na farko da kotun ta ɗauka shi ne jingine aiki da sabuwar dokar masarautar Kano ta 2024 wadda gwamnati mai ci ta yi.

"Kotu ta yi umarnin cewa a soke duk wani mataki da aka ɗauka na fara aiki da sabuwar dokar masarauta ta 2024.
"Abu na biyu kuma shi ne cewa hakan bai shafi inganci ko rashin ingancin dokar ba, saboda batun ne da har yanzu yake gaban kotu.”
"Saboda haka a doka yanzu haka Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano."

- Abba Hikima.

Lauyan ya ƙara da cewa duk da alkali bai soke dokar ba amma ya wajabta daina amfani da ita, wanda hakan ke nufin Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano.

Kano: Abubuwa 5 game da hukuncin kotu

A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta soke matakin dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Sai dai akwai muhimman bayanai a cikin hukuncin da ya kamata a ce kun sani, Legit Hausa ta tattaro maku su domin ku fahimci inda aka dosa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262