Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Gwamna Ya Kori Shugaban Majalisar Sarakuna

Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Gwamna Ya Kori Shugaban Majalisar Sarakuna

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sallami shugaban Majalisar sarakuna a jihar ana tsaka da rikicin siyasa
  • Fubara ya ce kori Chidi Awuse ne tare da maye gurbinsa da Eze Chike Worlu Wodo saboda zargin rashin iya shugabanci
  • Awuse ya kasance na hannun daman Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda ba su ga maciji da Gwamna Fubara a yanzu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya sallami shugaban Majalisar sarakunan gargajiya a jihar.

Simi Fubara ya kori Mai Martaba Chidi Awuse wanda ya kasance na hannun Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike.

Gwamna ya sallami shugaban Majalisar sarakuna a jiharsa
Gwamna Fubara ya kori shugaban Majalisar sarakuna wanda yake tare da Wike. Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Fubara ya kori na hannun daman Wike

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abba ya ba kwamishinan 'yan sanda sabon umarni kan fadar Nassarawa

Gwamnan ya maye gurbin Awuse da mai sarautar Apara, Eze Chike Worlu Wodo, Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, gwamnan ya ce ya sauya Awuse saboda rashin shugabanci mai inganci a matsayin mai jagorantar Majalisar sarakunan..

Sabon shugaban Majalisar, Wodo ya kasance mai sarautar Apara da ke karamar hukumar Obio/Akpor a jihar, cewar Punch.

Fubara ya yi zargin rashin iya shugabanci

Simi Fubara ya ce Majalisar sarakunan ta buga kalanda na shekarar 2024 inda ta ci mutuncin gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ce Majalisar yt ki saka hotunan gwamnan jihar da kuma mataimakinsa wanda hakan kaskanci ne.

Ya ce hakan ya tabbatar da cewa Majalisar ba za ta iya gudanar da shugabanci yadda ya kamata ba.

Jawabin gwamna Fubara na korar Awuse

"Na lura Majalisar sarakunan ba ta iya gudanar da shugabanci yadda yadda ya kamata, babu shugabanci nagari."

Kara karanta wannan

Zargin rashin caccakar ƴan adawa: Gwamna ya fatattaki sakataren yaɗa labaransa

"Ina son jan hankalinku kan cin mutunci da aka yiwa gwamnatin jiha, Majalisar ta buga kalanda ta 2024 amma babu hoton gwamna da mataimakinsa a ciki."

- Siminalayi Fubara

Fubara ya umarci binciken tsofaffin ciyamomi

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya umarci binciken tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Rivers.

Fubara ya dauki matakin ne yayin da ake zargin tsofaffin ciyamomin da almundahana lokacin da suke mulki a gwamnatin da ta shude.

Hakan ya biyo bayan karewar wa'adin ciyamomin 23 a ranar 17 ga watan Yunin 2024 bayan shafe shekaru kan mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.