El Rufai vs Uba Sani: Masu Zanga Zanga Sun Dira Gidan Gwamnatin Kaduna

El Rufai vs Uba Sani: Masu Zanga Zanga Sun Dira Gidan Gwamnatin Kaduna

  • Wasu masu zanga-zanga sun dira a gidan gwamnatin Kaduna domin neman a cafke tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai
  • Masu zanga-zangar ƙarƙashin ƙungiyar Kaduna Citizens Watch for Good Governance (KCWGG) sun buƙaci Uba Sani ya haɗa El-Rufai da EFCC
  • Shugaban ƙungiyar ya koka kan yadda rahoton kwamitin bincike kan gwamnatin El-Rufai ya bankaɗo yadda aka karkatar da maƙudan kuɗaɗe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - An gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar Kaduna domin neman a cafke Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Masu zanga-zangar ƙarkashin ƙungiyar Kaduna Citizens Watch for Good Governance (KCWGG) sun mamaye gidan gwamnati da ke Kaduna, domin neman a binciki tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai tare da kama shi.

Kara karanta wannan

Hukumar NAHCON ta ba Alhazan Najeriya umarni yayin da suke shirin dawowa gida

An yi zanga-zangar neman cafke El-Rufai a Kaduna
Masu zanga-zangar na son Gwamna Uba Sani ya binciki El-Rufai Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Uba Sani: Ana neman a cafke El-Rufai

Sun buƙaci Gwamna Uba Sani da ya gayyaci jami’an EFCC domin su kama El-Rufai tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin gwamnatinsa da karkatar da Naira biliyan 423, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙoƙi tare da ɗaga alluna da kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce daban-daban na neman a binciki El-Rufai.

Meyasa aka yi zanga-zangar El-Rufai?

Jaridar Leadership ta ce shugaban ƙungiyar masu zanga-zangar, Kwamared Victor Duniya ya zanta da manema labarai bayan sun isa gidan gwamnatin jihar Kaduna.

"Mun gode da zuwanku wajen nan yayin da muke nuna fushinmu. Jiharmu ta fuskanci rashin iya sarrafa kuɗaɗe, rashin iya mulki da ɗumbin bashi cikin shekara takwas da suka wuce."
"Babban abin takaici shi ne yadda aka gano an karkatar da N10.5bn na aikin ma'aikatar sarrafa madara a Damau a ƙaramar hukumar Kubau zuwa gina babban kantin Galazy Mall a Kaduna."

Kara karanta wannan

El-Rufai ya yi magana kan binciken da ake yi masa, ya fadi makomar Uba Sani a Kaduna

"Hakazalika rahoton ya kuma bankaɗo yadda aka riƙa cikawa ƴan kwangiloli kuɗade, biyan kuɗaɗe ga kamfanoni marasa rajista da biyan kuɗaɗen ayyukan da ba a kammala ba waɗanda sun kai sama da N36.5bn"

- Kwamared Victor Duniya

Batun binciken El-Rufai a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi martani kan zargin badaƙala da ake yi kan gwamnatinsa.

Tsohon ministan na birnin tarayya Abuja ya yi fatali da rahoton majalisar dokokin jihar kan binciken gwamnatinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel