Zargin Rashin Caccakar Ƴan Adawa: Gwamna Ya Fatattaki Sakataren Yaɗa Labaransa

Zargin Rashin Caccakar Ƴan Adawa: Gwamna Ya Fatattaki Sakataren Yaɗa Labaransa

  • Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya dauki mataki kan sakataren yada labaransa, Kazie Uko a jiya Laraba 19 ga watan Yuni
  • Otti ya sallami Uko tare da maye gurbinsa cikin gaggawa da Njoku Ukoha domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai a jihar, Okey Kanu ya fitar a jiya Laraba 19 ga watan Yuni

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya fatattaki sakataren yada labaransa, Kazie Uko.

Otti ya tabbatar da sallamar Uko ne ta bakin kwamishinan yada labarai, Okey Kanu a jiya Laraba 19 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Alhazai 600 ƴan ƙasa 1 sun mutu a Saudiyya, an gano silar ajalinsu

Gwamna ya sallami kakakinsa kan rashin katabus
Gwamna Alex Otti ya kori sakataren yada labaransa a jihar Abia. Hoto: Alex Otti.
Asali: Facebook

Abia: Gwamna Otti ya nada sabon kakakinsa

Gwamnan ya nada Iko wanda ɗan jarida ne a watan Yunin 2023 wata daya bayan hawa karagar mulkin jihar a cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani gwamnan ya naɗa Njoku Ukoha nan take domin maye gurbin Uko da aka sallama daga mukaminsa a jihar.

Duk da ba a bayyana dalilin korar Uko ba, wata majiya ta bayyanawa Premium Times musabbabin daukar matakin da gwamnan ya yi.

Musabbabin korar kakakin gwamnan Abia

Majiyar ta ce Otti ya sallami Uko ne saboda rashin gudanar da aikinsa da aka naɗa shi.

Ana zargin Uko ba ya caccakar ƴan adawa da sauran masu kushe ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

"Abin da suke bukata shi ne caccakar mutane, idan ba ka yin haka to ba ka yin aikin da aka dauke ka."

Kara karanta wannan

Ana daf da zabe, PDP ta sallami tsohon mataimakin gwamna da jiga-jiganta 2

- Majiyar

Har ila yau, wata majiya da ta bukaci boye sunanta ta ce ana zargin Uko ba ya ba ƴan jaridu dama idan suka bukaci hira da shi.

Gwamna zai binciki korarrun ciyamomi

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya ba da umarnin bincikar tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi 23 a jihar.

Fubara ya bukaci hakan ne domin tabbatar da gano yadda korarrun ciyamomin suka gudanar da mulkinsu a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan karewar wa'adin shugabanninsu kananan hukumomin da ya jawo rikici har da rasa rayuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.