Sallah: Atiku Ya Kai Ziyara ga IBB da Janar Abdulsalami a Minna, Hotuna Sun Bayyana

Sallah: Atiku Ya Kai Ziyara ga IBB da Janar Abdulsalami a Minna, Hotuna Sun Bayyana

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a inuwar PDP ya kai ziyarar barka da Sallah ga IBB da Abdulsalami Abubakar a Minna, jihar Neja
  • Atiku Abubakar ya bayyana haka a shafinsa ranar Laraba, 19 ga watan Yuni kwanaki kaɗan bayan hawan idin Babbar Sallah
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jima yana neman mulkin Najeriya amma har yanzu Allah bai ba shi ba kuma yana da niyyar sake takara a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ziyarar Barka da Sallah.

Haka nan kuma Wazirin Adamawa ya wuce ya kai gaisuwar Barka da Sallah ga tsohon shugaban ƙasa, Abdulsalami Abubakar.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Atiku Abubakar.
Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci IBB da Abdulsalami Abjbakar a Minna Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Atiku Abubakar ya kai wa waɗannan tsofaffin shugabannin ziyara ne har gidajen su da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ya tabbatar da haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a ranar Laraba.

Atiku ya ziyarci IBB da Abdulsalami

Atiku ya kuma wallafa hotunan ziyarar da ya kai wa jiga-jigan biyu domin taya su murnar bikin Babbar Sallah wadda aka yi ranar Lahadin da ta gabata.

"A yau na samu kai ziyarar barka da Sallah ga tsofaffin shugabanni, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) da Janar Abdulsalami Abubakar a gidajensu da ke Minna a jihar Neja."

Atiku da takarar shugaban kasa

Atiku shi ne dan takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023 da ya gabata.

Kara karanta wannan

PDP ta tsoma baki kan rikicin Ribas, yayin da APC ke neman a sanya dokar ta baci

Sai dai ya sha ƙasa a hannun Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a zaɓen wanda aka kai ruwa rana tsakanin manyan ƴan takara uku.

Dubban ƴan PDP sun koma APC

A wani rahoton na daban, an ji 'yan babbar jam'iyyar adawa PDP sama da 4,000 sun tattara kayansu sun koma jam'iyyar APC mai mulki a jihar Benuwai.

Gwamna Hyacinth Alia ne ya karɓe su da kansa a wani taro da aka shirya lokacin da yake zagayen godiya ga al'ummar jihar da suka zaɓe shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262