Kano: NNPP Tayi Martani, Ta Ce APC Na Yunƙurin Kwace Mulki Daga Gwamna Abba

Kano: NNPP Tayi Martani, Ta Ce APC Na Yunƙurin Kwace Mulki Daga Gwamna Abba

  • Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta zargi APC da yunƙurin kwace mulki ta kowane hali a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma
  • A wata sanarwa da kakakin NNPP na ƙasa ya fitar, jam'iyyar ta tona yadda APC ke amfani da shari'a da jami'an tsaro don tayar da zaune tsaye a jihar
  • Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan APC ta buƙaci jami'n tsaro su kama jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - New Nigeria People’s Party (NNPP) da jam'iyyar APC sun fara musayar yawu da zargin juna game da rikicin da ke faruwa a jihar Kano.

Awanni bayan APC ta buƙaci a kama Rabiu Kwankwaso saboda kalaman da ya yi, NNPP ta fito ta caccaki jam'iyyar da cewa ta cika ƙwaɗayin mulki.

Kara karanta wannan

Ganduje ya ƙara rusa ƴan adawa, manyan jiga-jigai da dubban mutane 4450 sun koma APC

Ganduje, Kwankwaso da Abba.
NNPP ta zargi APC da yunƙurin kwace mulkin Kano ta kowane hali Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jam'iyyar NNPP ta soki APC a Kano

NNPP mai kayan marmari ta zargi APC da yunƙurin kwace mulki da ƙarfi daga hannun zaɓin al'umma, Gwamna Abba Kabir Yusuf, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyya mai mulkin Kano ta yi wannan zargi ne a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson ya fitar yau Laraba.

A cewarta, matakin sauya dokar masarautar Kano da mayar da Muhammadu Sanusi II kan mulki ya ƙara fito da yadda APC ke tsananin son mulki.

APC na koƙarin hana Abba mulki

Jam’iyyar NNPP ta kuma yi zargin cewa APC na amfani da bangaren shari’a da jami’an tsaro wajen gurgunta tsarin dimokuradiyya da tada zaune tsaye a jihar.

Ta yi kira ga ƴan Najeriya su farka daga barci kana su toshe duk wata hanya da APC ke kokarin bi domin wargaza zaman lafiyar Kano da ƙwace mulki ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara tsanani, APC ta buƙaci Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jiha 1

A sanarwar, NNPP ta ce:

"APC ba ta ɓoye mugun nufinta na hana wanda ya lashe zaɓen 18 ga watan Maris, 2023, Abba Kabir Yusuf gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali ba."
"Yaushe aka tuge gwamna daga matsayin shugaban tsaron jiharsa? Mutanen Kano ba za su bari wanda suka zaɓa ya wulaƙanta ba, za su kare shi duba da abubuwan alherin da yake zuba masu."

- NNPP

Channels tv ta kawo rahoto cewa APC ta buƙaci jami'an tsaro su cafke jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso bisa zargi barazana ga tsaron Kano.

An bukaci Tinubu ya naɗa minista

A wani rahoton kuma Naƙasassu a jam'iyyar APC ta Kudu maso Yamma sun miƙa wa Bola Tinubu sunan wanda ya kamata ya naɗa a matsayin ministan jin ƙai.

Sun bukaci shugaban ƙasa ya naɗa sabon ministan jin ƙai ne yayin da suka kai masa ziyarar Barka da Sallah a jihar Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262