Shehu Sani Ya Fadawa Tinubu Ido da Ido Kuskuren da Ya Yi a Hada Kan ’Yan Kasa

Shehu Sani Ya Fadawa Tinubu Ido da Ido Kuskuren da Ya Yi a Hada Kan ’Yan Kasa

  • Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yadda zai hada kan 'yan Najeriya
  • Shehu Sani ya ce taken Najeriya ko kundin tsarin mulki ba za su hada kai ba sai dai adalci da samar da daidaito
  • Sanatan ya fadi haka ne a taron liyafar cin abinci a daren jiya Laraba 12 ga watan Yuni domin bikin dimukradiyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanata Shehu Sani ya magantu kan yadda Bola Tinubu zai a hada kan Najeriya cikin sauki a halin da ake ciki.

Sani ya ce taken Najeriya kadai ba zai taba hada kan 'yan kasar ba duba da yadda lamura suka lalace.

Kara karanta wannan

Abin farin ciki: Wata ƙasar Afrika ta fara haƙo mai a karon farko, an samu bayanai

Shehu Sani ya shawarci Tinubu kan yadda zai hada kan Najeriya
Shehu Sani ya fadawa Tinubu hanyoyin hada kan 'yan Najeriya. Hoto: Shehu Sani, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Sani ya fadi sharudan hada kan kasa

Shehu Sani ya ce 'yanci da adalci da kuma daidaito su ne kadai za su hada kan 'yan kasar cikin sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya bayyana haka ne a faifan bidiyo yayin liyafar cin abinci domin bikin dimukradiyya a Abuja a jiya Laraba 12 ga watan Yuni.

"Mai girma shugaban kasa, ina son amfani da wannan dama domin jan hankalinka kan wannan lamari, taken Najeriya ba shi ne zai hada kan Najeriya ba."
"Taken Najeriya ko kundin tsarin mulki ba za su kawo hadin kai ba sai dai adalci da daidaito da kuma samar da 'yanci a kasa."
"Dimukradiyya ba kyauta ba ce daga sojoji kuma ba a caca muka yi nasara ba sai dai jajircewa da sadaukar da kai na wasu 'yan Najeriya."

- Shehu Sani

Sani ya shawarci Tinubu kan daga darajarsa

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya bayyana nasara 1 da Najeriya ta samu saboda dimokuraɗiyya

Shehu Sani ya ce idan Tinubu ya yi nasara za a yaba masa saboda ya yi gwagwarmaya tun farko a siyasa.

Ya ce amma idan ya gaza za a iya cewa wadanda suka kawo dimukradiyya ba su tsinanawa kasar komai ba.

Wannan na zuwa ne yayin da aka gudanar da bikin dimukradiyya a jiya Laraba 12 ga watan Yuni bayan dawowarta a shekarar 1999.

Atiku ya jajantawa Tinubu a Abuja

Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nuna damuwa bayan Bola Tinubu ya zame a taro.

Atiku ya jajntawa shugaban inda ya masa fatan yana lafiya bayan tsautsayin da ya afku da shi a Eagle Square.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.