Ana Shirin Babbar Sallah, Gwamna Ya Dakatar da Wasu Manyan Hadimai 3 Daga Aiki

Ana Shirin Babbar Sallah, Gwamna Ya Dakatar da Wasu Manyan Hadimai 3 Daga Aiki

  • Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wasu manyan jami'ai daga aiki bisa zargin amfani da takardun bogi da kuma satar kuɗin talakawa
  • Hukumar kula da ma'aikata ta jihar ce ta bayyana haka a wata sanarwa ranar Laraba bayan kammala taronta karo na 21
  • Ta kuma amince da naɗin sababbin daraktoci da mataimakansu na rikon kwarya domin inganta ayyukan wasu ma'aikatu a Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta dakatar da wasu manyan jami'anta guda uku.

Hukumar kula da ma'aikatan jihar Bauchi ce ta dakatar da manyan jami'an bisa zargin amfani da takardun bogi da kuma almundahana.

Gwamna Bala Mohammed
Gwamnatin Bauchi ta dakatar da manyan jami'ai uku daga aiki Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: Facebook

Gwamna ya dakatar da jami'ai a Bauchi

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Rahoton Leadership ya tattaro cewa waɗanda aka dakatar sun haɗa da babban Akanta na ma'aikatar lafiya, Yakubu Muhammad.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran su ne babban jami’in gudanarwa na sashen baitul-malin Bauchi, Surajo Shehu Ilela, da mataimakin jami’in gudanarwa na hukumar harkokin sadarwa, Umar Muhammad Misau. 

Tuni dai gwamnatin Bauchi ta janye naɗin da aka yiwa Umar Misau, har sai an kammala bincike kan zarge-zargen da ke kansa.

Meyasa gwamna ya dakatar da ma'aikatan?

An tattaro cewa laifukan da ake zargin jami'an uku da aikatawa sun sabawa tanadin dokokin aikin gwamnati mai lamba 0327 (a) da (b) bi da bi.

Jami’in yada labarai na hukumar kula da ma’aikata ta jihar Bauchi, Saleh Umar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Bauchi ranar Laraba.

An naɗa sababbin daraktoci a Bauchi

Kara karanta wannan

Tinubu ya gama shirin garambawul, zai tsige wasu ministoci da kirkiro sabuwar ma'aikata

Ya ce an tattauna batun dakatarwar kuma an amince da shi a wurin babban zaman hukumar da ya gudana karo na 21, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

A daya bangaren kuma, Umar ya ce hukumar ta yi nazari tare da amincewa da nadin sababbin daraktoci hudu da mataimakan daraktoci biyu na rikon kwarya.

Jonathan ya soki wasu gwamnoni

A wani rahoton kun ji cewa Dokta Goodluck Ebele Jonathan ya zargi wasu gwamnonin jihohi da amfani da ƴan daba wajen maguɗin zaɓe don cimma burinsu na siyasa

Tsohon shugaban ƙasar ya ce maimakon gwamnoni su gina matasan ta hanyar da gwamnati za ta amfana da su, sun zaɓi mayar da su ɓata gari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel