"Mene Nayi Muku?": Sanata Ta Koka Kan Mayar da Ita Saniyar Ware a Mazaɓarta kan Kudi

"Mene Nayi Muku?": Sanata Ta Koka Kan Mayar da Ita Saniyar Ware a Mazaɓarta kan Kudi

  • Sanata mai wakiltar birnin Abuja, Ireti Kingibe ta yi korafi kan yadda aka ware ta kan lamuran da suka shafi mazaɓarta
  • Ireti ta nuna damuwa kan yadda aka mayar da ita saniyar ware a harkokin Majalisar da ya shafi Abuja musamman kasafin kudi
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake gabatar da kasafin kudi N98.5bn karo na biyu na birnin Abuja a gaban Majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanata Ireti Kingibe da ke wakiltar birnin Abuja ta koka kan yadda aka mayar da ita saniyar ware.

Ireti Kingibe ta nuna damuwa kan yadda ake nuna mata wariya a kwamitocin da suka shafi mazaɓarta.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara binciken yawaitar hadurran jirgin kasa a Najeriya

Sanata ta koka kan nuna mata wariya a mazabarta
Sanata Ireti Kingibe ta nuna damuwa kan mayar da ita saniyar ware a mazabarta. Hoto: @ireti_kingibe, @GovWike.
Asali: Twitter

Abuja: Sanata Ireti ta koka a Majalisa

Sanatar ta bayyana haka ne a yau Talata 11 ga watan Yuni a dakin Majalisar, kamar yadda Punch ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce ita ce mafi girma a birnin da aka zaba gaba daya amma kwata-kwata ba a damawa da ita kan lamuran da suka shafi birnin a cewar TheCable.

"Mai girma shugaban Majalisa, na fi kowa a girma a cikin wadanda aka zaba a birnin Abuja da mutane fiye da miliyan hudu."
"Kwata-kwata ba a saka ni cikin lamuran birnin Abuja musamman harkar kasafin kudi."
"An gabatar da kasafin kudi na Abuja karo na biyu amma ban san komai a kai ba, babu wata ganawa kan lamarin da aka tuntube ni."

- Ireti Kingibe

An mikawa majalisa karin kasafin kudin Abuja

Wannan martanin nata na zuwa ne yayin gabatar da karin kasafin kudin Abuja kimanin N98.5bn a Majalisar.

Kara karanta wannan

Wike na cikin alheri dumu dumu: Majalisa ta amince da ƙarin N98.5bn a kasafin Abuja

Sai dai shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya dakatar da ita inda ya bukaci ta kawo korafi a Majalisar.

Sanata Kingibe ta caccaki Wike a Abuja

Kun ji cewa Sanatar da ke wakiltar birnin Tarayya Abuja, Ireti Kingibe ta gargaɗi Ministan birnin, Nyesom Wike kan wuce gona da iri.

Kingibe ta soki Wike ne kan nadin sakatarori a hukumar FCTA ba tare da tuntuɓar Majalisar Tarayya ba.

Ta bayyana cewa Majalisar Tarayya ita ce za ta gudanar da ayyukan Majalisa na hukumar babban birnin Tarayya (FCTA) kamar yadda Majalisar Dokoki ta jiha ke yiwa gwamnatin jiha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.