"Ba Za Ku Ci Banza Ba": An bukaci Gwamna Ya Binciki Ciyamomi Masu Barin Gado

"Ba Za Ku Ci Banza Ba": An bukaci Gwamna Ya Binciki Ciyamomi Masu Barin Gado

  • Kungiyar Rivers Development Foundation (RiDeF) ta bukaci Gwamna Sim Fubara ya binciki shugabannin kananan hukumomi
  • Kungiyar ta ce akwai manyan zarge-zarge kan shugabannin kananan hukumomin da ke shirin barin mulki wanda ya shafi asusun jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin a bangaren shugabannin kananan hukumomin suka zargi Fubara da rike musu makudan kudi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Kungiya a jihar Rivers ta bukaci Gwamna Siminalayi Fubara ya binciki shugabannin kananan hukumomi masu barin gado.

Kungiyar Rivers Development Foundation (RiDeF) ta ce akwai zargin karkatar da kudi daga asusun ƙananan hukumomi kan shugabannin.

Ana zargin shugabannin kananan hukumomi da kwashe kudin jiha
Kungiya ta shawarci Gwamna Sim Fubara ya binciki shugabannin kananan hukumominsa. Hoto: Siminalayi Fubara.
Asali: Twitter

Rivers: An zargi ciyamomi da kassara jiha

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Juma'a 7 ga watan Yuni, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Ana daf da gudanar da zabe, 'yan bindiga sun harbe jigon dan takarar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar kungiyar, Rejoice Okoli ta bukaci Fubara ya kafa kwamitin bincike domin bankado badakalar ciyamomin, Punch ta tattaro.

"Kungiyar RiDeF tana kira ga Gwamna Siminalayi Fubara kan zargin badakala a shugabancin kananan hukumomi."
"Akwai manyan zarge-zarge kan shugabannin kananan hukumomin jihar masu jiran gado."
"Muna rokon Fubara ya kada kwamitin bincike saboda girman zarge-zarge wanda ya daga hankalin mutanen jihar Rivers."

- Rejoice Okoli

Rivers: Shugaban karamar hukuma ya kalubalanci Fubara

Wannan na zuwa ne bayan wani daga cikin shugabannin kananan hukumomi ya kalubanci gwamnan jihar kan wa'adinsa.

Shugaban karamar hukumar Ikwerre, Dakta Samuel Nwanosike ya sha alwashin ci gaba da zama a kujerarsa.

Nwanosike ya gargadi Gwamna Sim Fubara kan shirin da ya ke yi a kansu inda ya ce babu mai cire shi a kujerarsa.

Shugaban karamar hukumar ya ce shi bai aminta da wa'adin da gwamnan ya ba su na ranar 16 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

El-Rufai: PDP ta haɗa baki da Uba Sani kan zargin tsohon gwamna, ta nemo mafita

Fubara ya sallami ma'aikata 10,000 na Wike

Kun ji cewa rikicin siyasar jihar Rivers ya sake rikidewa bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya ballo aiki.

Sim Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya yi a lokacin mulkinsa.

Gwamnan ya ce bai amince da yadda aka bi tsarin daukar aikin ba inda ya ce akwai kura-kurai a ciki inda ya ce zai sake daukar wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.