Kano: Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ya Dauke Hankalin Abba a Shekara 1 Na Mulki

Kano: Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ya Dauke Hankalin Abba a Shekara 1 Na Mulki

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya magantu kan irin kokarin 'yan adawa na kawo rudani a jihar a mulkin Abba Kabir
  • Kwankwaso ya zargi jam’iyyun adawa da neman dagula jihar bayan kammala zaben inda suka shiga kotu domin kalubalantar zaben
  • Sanatan ya bayyana haka ne a yau Asabar 8 ga watan Yuni a birnin Kano yayin sanya dokar ta baci a bangaren ilimi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana wadanda suke kawo rudani a jihar Kano musamman a mulkin Abba Kabir Yusuf.

Kwankwaso ya ce makiya jihar Kano ne suke kawo tarnaki domin kauda hankalin gwamnatin jihar cikin shekara daya da ta yi.

Kara karanta wannan

Alhazan Kano sun samu gata, an fara ciyar da su abinci kyauta a Saudiyya

Kwankwaso ya yabawa mulkin shekara 1 na Abba Kabir a Kano
Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana ci gaba da Abba Kabir ya kawo a Kano. Hoto: Rabiu Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kano: Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir

Sanatan ya bayyana haka ne a yau Asabar 8 ga watan Yuni yayin taron tabbatar da dokar ta baci a bangaren ilimi a jihar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Zan fara da taya shi murna kan wannan rana mai tarihi, ranar da ake sanya dokar ta baci a bangaren ilimi.”
“Wadanda ba su sani ba, gwamnan yana aiki ba dare ba rana domin inganta jihar kamar yadda kuke gani ya tabo ko ina.”
“Duk da yawan dauke hankalinsa da aka yi na shekara daya, bayan kammala zabe, makiya Kano sun maka shi a kotu, mun ga abin da ya faru duk sun sani babu bukatar zuwa kotu saboda kowa ya sani shi ya ci zabe.”

- Rabiu Kwankwaso

'Sun nemi kwace mulki da karfi" - Kwankwaso

Kwankwaso ya ce hatta su ma makiyan suna cewa za su kwace mulkin ne da karfi saboda suna da gwamnati.

Kara karanta wannan

Mutane 8 sun mutu yayin da aka yi asarar dukiyar da ta kai N31.6m a jihar Kano

Ya ce duk da matsalolin da ya fuskanta, Abba ya gudanar da ayyukan alheri ga 'yan jihar Kano.

Kwankwaso ya magantu kan matsalolin Arewa

Kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana rashin shugabanci a matsayin babbar matsalar Arewa.

Kwankwaso ya koka kan yadda ake yaudarar mutane a zabe domin zabar azzalumai wurin ba su taliya da atamfa.

Sanatan ya bayyana burinsa na kawo karshen matsalar tsaro da zarar ya samu damar darewa shugabancin kasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel