Yaron Kwankwaso Ya Samu Shirgegen Mukami a Ketare, Ya Mika Godiya ga Sanata

Yaron Kwankwaso Ya Samu Shirgegen Mukami a Ketare, Ya Mika Godiya ga Sanata

  • Yaron Sanata Rabiu Kwankwaso ya samu mukamin shugaban Jami'ar Weldios a birnin Cotonou da ke Jamhuriyar Benin
  • Dakta Isaac Idahosa ya yi takarar mataimakin shugaban kasa ga Kwankwaso a jam'iyyar NNPP a zaben 2023 da aka gudanar
  • Idahosa ya yi godiya marar misaltuwa ga jagoran siyasar Kano inda ya ce ba zai taba mantawa da aminci da ke tsakaninsu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Cotonou, Benin - Mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Dakta Isaac Idahosa ya samu mukami a Jami'a.

Idahosa ya samu mukamin shugaban Jami'ar Weldios da ke birnin Cotonou a Jamhuriyar Benin.

Yaron Kwankwaso ya samu mukami a Jami'a
Mataimakin Rabiu Kwankwaso a zaben 2023, Isaac Idahosa ya zama shugaban Jami'a a Jamhuriyar Benin. Hoto: Bishop Isaac Idahosa.
Asali: Facebook

Fasto Idahosa ya godewa hukumomin Jami'ar Benin

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa Bola Tinubu ya fi Atiku da Obi cancantar zama shugaban ƙasa a 2023"

Fasto Idahosa ya kasance mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a zaben 2023, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idahosa ya yi godiya matuka ga hukumomin Jami'ar da suka duba dacewarsa kan wannan mukami da ya samu.

Ya bayyana hakan da taimako daga Ubangiji inda ya ce zai dauki hukuncin da hannu bibbiyu.

Idahosa ya yi godiya ga Sanata Kwankwaso

"Ina matukar godiya ga Ubangiji da samun wannan dama, wannan dama ce da zan kara yada kalmar ubangiji ga jama'a."
"Ina godiya marar misaltuwa ga shugabanmu, Sanata Rabiu Kwankwaso duba da irin yarda da ya nuna mini da amincewa da ni."

- Isaac Idahosa

Idahosa ya yi alkawarin hada kai masu ruwa da tsaki a Jami'ar domin kawo sauyi da zai bunƙasa ilimi a cikinta.

Ya ce hakan zai ba kowa damar ba da tashi gudunmawa kama daga ɗalibai da ma'aikata da sauran jami'ai.

Kara karanta wannan

Duk da umarnin sammaci, Ganduje ya yi biris, ya kaddamar da muhimmin aiki ga APC

Kwankwaso ya magantu kan matsalar Arewa

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana babbar matsalar da ke damun yankin Arewacin Najeriya.

Kwankwaso ya ce rashin shugabanci nagari shi ne matsalar da yankin ke fama da shi kama daga rashin tsaro da talauci da kuma rugujewar tattalin arziki.

Ɗan takarar shugaban kasar a zaben 2023 ya koka kan yadda aka yaudari mutane a zaben da taliya da atamfa inda suka zabi azzalumai a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.