Gwamna Ya Tsige Shugaban Karamar Hukuma da Mataimakinsa, Ya Tura Masu Saƙo

Gwamna Ya Tsige Shugaban Karamar Hukuma da Mataimakinsa, Ya Tura Masu Saƙo

  • Gwamna Bala Mohammed Ƙauran Bauchi ya tsige shugaban ƙaramar hukumar Alkaleri, Hon Bala Ibrahim tare da mataimakinsa
  • Sakataren gwamnatin Bauchi, Barista Ibrahim Kashim Mohammed ya sanar da haka a wata takarda da ya tura ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautu
  • Duk da ba a faɗi dalilin korar ba, gwamnan ya umarci mutanen biyu su ajiye kayan gwamnati da ke hannun su sannan su bar ofis nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya tsige shugaban ƙaramar hukumar Alkaleri na rikon kwarya watau kantoma, Hon Bala Ibrahim.

Gwamna Bala ya tsige kantoman tare da mataimakinsa kan wasu dalilai da har kawo yanzun ba a bayyana ba.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 da manyan jiga-jigai sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a Abuja

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed Kauran Bauchi.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya kori kantoma da mataimakinsa a ƙaramar hukumar Alkaleri Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata takardar kora mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin Bauchi, Barista Ibrahim Kashim Mohammed, jaridar Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamnan Bauchi ya kori kantoman?

Ƙauran Bauchi ya umarci kantoman da mataimakinsa su gaggauta mika harkokin mulki ga shugaban sashin gudanarwa na ƙaramar hukumar Alƙaleri.

Takardar na ɗauke da kwanan watan jiya Alhamis, 6 ga watan Yuni, 2024 kuma an mata taken, "An sallami kantoma da mataimakinsa na ƙaramar hukumar Alƙaleri."

Barista Ibrahim ya aika da takardar sallamar ne ga babban sakatare na ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jihar Bauchi.

Wani sashin sanarwar ya ce:

"Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed na jihar Bauchi ya amince da sallamar kantoma da mataimakinsa na ƙaramar hukumar Alkaleri nan take.
"Saboda haka ana umartarka da ka faɗawa waɗanda korar ta shafa su mika dukkan kayayyakin da ke hannunsu ga shugaban sashin gudanarwa na ƙaramar hukumar."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya bankaɗo 'dalilin' ɓoye ɓoyen gwamanti kan tallafin fetur

Sai dai sanarwan ba ta bayyana ainihin dailin da ya sa Gwamna Bala ya kori shugabannin biyu ba.

Gwamnoni sun gana kan ƙarin albashi

A wani rahoton gwamnonin jihohin Najeriya sun yi taro kan mafi ƙarancin albashi yayin da kwamitin da aka kafa ke ci gaba da tattaunawa da ƴan kwadago.

Wata majiya ta bayyana cewa gwamnoni ba za su iya biyan abin da ya haura N70,000 ba bisa la'akari da yanayin tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262