Gwamnoni Sun Yanke Shawarar Mafi Ƙarancin Albashin da Za Su Iya Biyan Ma'aikata

Gwamnoni Sun Yanke Shawarar Mafi Ƙarancin Albashin da Za Su Iya Biyan Ma'aikata

  • Gwamnonin jihohin Najeriya sun yi taro kan mafi ƙarancin albashi yayin da kwamitin da aka kafa ke ci gaba da tattaunawa da ƴan kwadago
  • Wata majiya ta bayyana cewa gwamnoni ba za su iya biyan abin da ya haura N70,000 ba bisa la'akari da yanayin tattalin arziki
  • A kwanakin baya Gwamna AbdulRazaq na jihar Kwara ya sanar da cewa jihohi za su biya ƙarin albashi daidai da aljihunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnonin jihohi a Najeriya sun bayyana adadin da za su iya biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a loƙacin da ake ci gaba da tattaunawa.

A wani taro da suka yi a Abuja jiya Alhamis, shugabannin jihohin sun yi duba tare da nazari kan yanayin tattalin arziƙi, inda suka karƙare da ba za cewa ba za su iya biyan abin da ya haura N70,000 ba.

Kara karanta wannan

A ina gwamnan Edo ya ga N70,000 na mafi karancin albashi? Shehu ya taso gwamnoni a gaba

Taron gwamnonin jihohi.
Gwamnoni ba za su iya biyan abinda ya haura N70,000 a albashi ba Hoto: Abdulrahman AbdulRazaq
Asali: Twitter

Gwamnoni ba za su biya N100, 000 ba

Kamar yadda The Nation ta tattaro, gwamnonin sun yi fatali da tayin N100,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi kamar yadda wasu ke yaɗawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa gwamnonin sun yi zama a Abuja karƙashin ƙungiyarsu NGF domin duba buƙatar ƴan kwadago.

Albashi: Gwamnoni sun fara ɗaukar matsaya

Sun yi nazari kan tayin N60,000 da gwamnatin tarayya ta gabatar a baya da kuma N70,000 wanda gwamnatin jihar Edo ta fara biya a matsayin mafi ƙarancin albashi, cewar Channels tv.

Wata majiya a taron ta ce:

"Bayan dogon nazari kan mafi karancin albashi, mun yanke shawarar duba tsakanin N60,000 zuwa N70,000. Ba mu iya cimma matsaya ɗaya ba."

Kungiyar NGF ta kafa kwamitin karin albashi

Bayan sun gaza cimma matsaya guda kan ƙarin albashin, NGF ta kafa kwamiti karƙashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: 'Yan Najeriya sun gano tushen matsalolin kasa, sun ambaci suna

Uzodimma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin da aka zaɓa karƙashin inuwar All Progressive Congress watau APC mai mulkin ƙasa.

Matsayar gwamnonin ta jiya ya yi daidai da kalaman da shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya yi a baya.

Idan ba ku manta ba Gwamna AbdulRazaq ya ce jihohin za su amince kuma su fara biyan mafi karancin albashi idan bai wuce ƙima ba.

Minista ya miƙa lissafin albashi ga Tinubu

Rahoto ya zo cewa Ministan kudi, Wale Edun ya miƙawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu rahoton sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ministan tattalin arzikin arzikin wa'adin sa'o'i 48 ya tattara bayanai ya miƙa masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262