Rikicin Siyasa Ya Ɓarke a Jam’iyyar Kwankwaso, NNPP Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna

Rikicin Siyasa Ya Ɓarke a Jam’iyyar Kwankwaso, NNPP Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna

  • Ana saura watanni uku a gudanar da zaben gwamnan Edo, jam'iyyar NNPP ta dakatar da ɗan takarar ta na gwamnan jihar, Azemhe Ezena
  • A wata sanarwa da jam'iyyar, reshen gundumar ɗan takarar ta fitar, an ji NNPP ta dakatar da Fasto Ezena ne saboda ayyukan zagon ƙasa
  • Sai dai ɗan takarar gwamnan ya ƙaryata wannan dakatarwar yana mai cewa aikin 'yan adawa ne wadanda ba halastattun 'yan jam'iyya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Edo - Rahotanni sun bayyana cewa rikicin siyasa ya barƙe a jam'iyyar NNPP mai alamar kwandon kayan marmari ta Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.

Ana saura watanni uku a gudanar da zaben gwamnan Edo, jam'iyyar NNPP ta dakatar da ɗan takarar ta na gwamnan jihar, Fasto Azemhe Azena.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2024: APC ta rasa babban jigon da take ji da shi, ya samu matsayi a NNPP

NNPP ta dakatar da dan takarar gwamnan Edo
Dan takarar gwamnan Edo ya ki amincewa da korar da NNPP ta yi masa. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jam'iyyar NNPP reshen gunduma ta 10 a karamar hukumar Etsako ta Kudu ne suka dakatar da Fasto Ezena, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta dakatar da dan takarar gwamna

A yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumba, an ce an dakatar da Fasto Ezena saboda zargin yiwa NNPP zangon ƙasa, da ƙin mutunta tsare-tsarenta.

Shugaban jam'iyyar na reshen gunduma ta 10, Kadiri Eshimokha; Sakataren jam'iyyar, Kwamred Imonikho Abdul; Shugabar mata, Misis Stella Afebua da shugaban matasa, Kwamred Eshiobo Johnson ne suka saka hannu a takardar dakatarwar.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa an miƙa takardar dakatarwar ga shugaban jam'iyyar na jiha, mataimakin jam'iyyar na ƙasa (shiyyar Kudu maso Kudu), da hukumar zaben jihar.

NNPP: Dan takarar gwamna ya yi martani

Sai dai a wani martani da ya yi kan wannan dakatarwa, dan takarar gwamnan jihar ya ce wannan shirin wasu 'yan hassada ne kawai, waɗanda ba 'yayan jam'iyyar ba ne.

Kara karanta wannan

Ana daf da zabe, ɗan takara a jam'iyyar Kwankwaso ya janye daga neman gwamna

Jaridar Daily Trust ta rahoto ɗan takarar gwamnan ya jaddada cewa shugaban jam'iyyar na gunduma ta 10 na asali, Goddy Iyamah ya ƙaryata dakatarwar.

"Mr Goddy Iyamah, ainihin shugaban jam'iyyar na gundumata ya ƙaryata wannan dakatarwa, kuma ya ce wadanda suka fitar da takardar ba 'yan jam'iyya ba ne."

- In ji Fasto Ezena.

Majalisa ta amince da nadin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta amince da nade-naden Shugaba Bola Tinubu a hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta ƙasa (SEC).

Majalisar ta amince da nadin Emomotimi Agama a matsayin babban darakta na hukumar tare da kwamishinoni uku, mata biyu da namiji daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.