Sanusi II Vs Aminu: Jerin Muhimman Wurare 4 da Gwamnatin Abba Ta Yi Kama da Ta Ganduje

Sanusi II Vs Aminu: Jerin Muhimman Wurare 4 da Gwamnatin Abba Ta Yi Kama da Ta Ganduje

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Har yanzu ana ci gaba da taƙaddama kan kujerar sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Alhaji Aminu Ado Bayero.

Masu sharhi kan lamarin na ganin wannan rikicin ya samo asali ne daga faɗan siyasa tsakanin tsoffin gwamnonin jihar, Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Ganduje.

Abdullahi Ganduje da Abba Kabir Yusuf.
Sanusi/Bayero: Gwamnatin Abba ta kama hanyar zama irin Gwamnatin Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A zaɓen 2023, Rabiu Kwankwaso ya jagoranci NNPP ta doke APC da ɗan takarar gwamna mai barin gado Abdullahi Ganduje da Nasiru Gawuna a zaɓen gwamna da aka yi a watan Maris.

Legit Hausa za ta tattaro muku irin wuraren da aka samu kamanceceniya tsakanin Gwamnatin Abba Kabir da magabacinsa Ganduje kan lamarin gidan sarauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ministoci 3 da manyan jiga-jigai sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a Abuja

1. Tsige Sarakuna

Abu na farko da zamu ɗauka shi ne sauya sarakuna, wanda babu shakka gwamnati mai ci da wadda ta shuɗe sun ɗauki matakai kusan iri ɗaya.

A rahoton Channels tv, tun farko Kwankwaso ya naɗa Muhammadu Sanusi II, tsohon gwamnan CBN a matsayin sarkin Kano na 14 ranar 9 ga watan Yuni, 2014.

Bayan Ganduje ya hau mulki, gwamnatinsa ta samu saɓani da masarautar Kano a lokuta daban-daban, lamarin da ya kai ga kirkiro sababbin masarautu domin rage ƙarfin Sanusi.

Ganduje ya rattaɓa hannu kan kudirin dokar da majalisar dokokin Kano ta zartar na raba masarautar Kano zuwa biyar a watan Disamba, 2019.

Gwamnatin Ganduje ta tsige Sanusi II bisa rashin mutunta umarnin doka sannan ta tura shi karamar hukumar Loko a jihar Nasarawa ranar 9 ga watan Maris, 2020.

A yanzu da Gwamna Abba Kabir ya karɓi mulki daga Ganduje, ya tsige sarakuna biyar da tsohon gwamnan ya naɗa bayan sauke Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

Zargin almundahana: Kotu ta yi umarnin buga sammacin shugaban APC, Ganduje a jaridu

Gwamnan ya sa hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano, 2024 wadda ta rushe dukkan masarautu, ta umarci a koma asali watau masarauta ɗaya.

2. Take umarnin kotu

Gwamna Abba ya bi sahun magaɓacinsa wajen take umarnin kotu musamman bayan mayar da Sanusi II kan kujerar sarkin Kano.

Idan za ku iya tunawa babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta umarci gwamnatin jihar ta dakatar da naɗin Sanusi da rushe masarautu biyar.

Sai dai duk da wannan umarni, Gwamna Abba ya miƙa wa Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki, inda ya sha alwashin kai ƙorafin alƙalin gaban ƙungiyar gwamnoni.

Kusan haka ta faru a mulkin Ganduje, babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin hana gwamnatin Kano aiwatar da dokar raba masarauta zuwa gida biyar.

Kotun ta bayar da umarnin ranar 10 ga watan Mayu, 2019 amma washe gari Ganduje ya rabawa sababbin sarakunan da ya naɗa takardar kama aiki.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, Sarki Sanusi II ya faɗi abin da zai kawo ci gaba a ƙasa

Ranar 12 ga watan Mayu, Gwamna Ganduje ya miƙa masu sandar mulki, watau dai ya sa kafa ya yi fatali da umarnin kotu, rahoton Independent.

3. Sauke sarki da naɗa sabo rana ɗaya

Ganduje ya sauke Sanusi II daga karagar mulki ranar 9 ga watan Maris, 2020, sannan ya tura shi ƙaramar hukumar Loko a jihar Nasarawa.

A wannan rana gwamnan ya sanar da naɗin Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Kano na 15 a tarihi.

Idan muka dawo kan Gwamna Abba, ya rattaɓa hamnu a kan dokar rushe masarautun da Ganduje ya ƙirƙiro a ranar 23 ga watan Mayu, 2024.

Jim kaɗan bayan haka gwamnan ya sanar da cewa ya mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarkin Kano.

4. Rashin sauraron jama'a

Ana ganin dukkan jiga-jigan biyu ba su sauraron ra'ayoyin jama'a musamman a abin da ya shafi masarautar Kano.

A lokacin da Ganduje ya sauke Sanusi II, manyan mutane a ƙasar nan sun sa baki domin sasanta saɓanin da ya shiga, amma hakan bai haifar da sakamako mai kyau ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sa tukuicin N25m ga duk wanda ya taimaka aka kama waɗanda suka kashe sojoji

Haka nan Gwamna Abba duk da ƴan Kano ba su ji daɗin abin da Ganduje ya yi ba a wancan lokacin, amma galibinsu suna ganin matakin da gwamnan ya ɗauka ya yi tsauri.

Lauyoyin sun gwabza a shari'ar Aminu Ado

A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta tanadi hukunci kan karar da mai martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya shigar.

Alkalin kotun , Mai shari’a Simon Amobeda, ya tanadi hukuncin biyo bayan zazzafar muhawara tsakanin lauyoyin kowane ɓangare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262