Tinubu Ya Fadi Ministan da bai Yi Nadamar Nada Shi ba a Gwamnatinsa, Ya Kora Yabo

Tinubu Ya Fadi Ministan da bai Yi Nadamar Nada Shi ba a Gwamnatinsa, Ya Kora Yabo

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yabawa Ministan Abuja, Nyesom Wike kan irin kokarin da ya ke yi a birnin tarayya
  • Tinubu ya ce Wike na daga cikin wandanda aka nada mukamai a gwamnatinsa wanda suka yi bajinta a shekara daya
  • Shugaban ya kora yabon ne ga Wike a yau Laraba 5 ga watan Yuni a Abuja wanda mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana mukamin da ya nada wanda bai yi nadama ba a gwamnatinsa.

Tinubu ya ce Ministan Abuja, Nyesom Wike shi ne mukami mafi kyau a cikin sauran mukaman da ya nada.

Kara karanta wannan

"A gwada matasa kawai": Tsohon shugaban kasa ya koka kan shugabancinsu

Tinubu ya yabawa Ministansa kan fice da ya yi a ayyukan raya kasa
Shugaba Bola Tinubu ya yabawa Nyesom Wike kan ayyukan alheri. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya kora yabo ga Wike

Shugaban ya bayyana haka ne a yau Laraba 5 ga watan Yuni a Abuja yayin kaddamar da wani babban aiki da Ministan ya yi, TheCable ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya wakilci shugaban ya yabawa Wike kan ayyukan da ya yi a Abuja, cewar Daily Post.

“Yayin da muke kaddamar da wannan aiki, ya kamata mu yabawa Wike kan kokarin da ya ke yi.”
“Ko ka so shi ko ka ki shi dole ne ka yaba masa saboda yana daga cikin mafi kyawu a wadanda Tinubu ya nada mukamai a gwamnatinsa.”
“Wike mutum ne mai son ci gaban mutane wanda ya kamata kowa ya yi koyi da shi domin inganta Najeriya.”

- Kashim Shettima

Tinubu ya yi godiya ga sauran mutane

Tinubu bayan yabon Wike ya kuma godewa sauran masu ruwa da tsaki da suka ba da gudunmawa wurin ayyukan ci gaba.

Kara karanta wannan

Abubuwan kunya 6 da suka faru da Gwamnatin Tinubu a cikin shekara 1

Wike na daga cikin Ministocin da wasu 'yan kasar ke yabo saboda irin ayyukan da yake yi babu kakkautawa.

Shettima ya fadi babbar matsalar Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana babbar matsalar Najeriya a yanzu.

Shettima ya ce kasar ba ta bukatar sauya tsarin mulki sai dai shugabanci nagari wanda zai kawo ci gaba a bangarori da dama.

Wannan na zuwa ne yayin da ake yawan kiraye-kiraye domin sauya tsarin mulki da ake yi yanzu a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel