Ganduje Ya Ƙara Gigita PDP, Ya Jawo Babban Jigon Siyasa Zuwa Jam'iyyar APC

Ganduje Ya Ƙara Gigita PDP, Ya Jawo Babban Jigon Siyasa Zuwa Jam'iyyar APC

  • Jam"iyyar PDP ta rasa tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Abia, Paul Taribo, wanda ya koma APC mai mulki
  • Hon. Taribu ya bayyana cewa ya zabi shiga APC ne domin haɗa kai da mambobi wajen ƙara tallata jam'iyyar gabanin zuwan zaɓen 2027
  • Tsohon ɗan majalisar ya ce lokaci ya yi da jihar Abia za ta rabu da tsagin adawa, ta koma inuwa ɗaya da jam'iyya mai mulkin ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Abia, Honorabul Paul Taribo ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Tsohon ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ekwa ta Gabas ya ce ya zaɓi shiga APC ne domin haɗa kai sauran ƴaƴanta wajen ƙara tallata tsintsiya gabanin 2027.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, Sarki Sanusi II ya faɗi abin da zai kawo ci gaba a ƙasa

Umar Damagum da Abdullahi Ganduje.
Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar Abia ya sauya sheka zuwa APC Hoto: Umar Damagum, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne jiya Talata, 4 ga watan Yuni, 2024 a hedkwatar APC da Umuahia, babban birnin jihar Abia, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Taribo ya koma APC?

Ya ce ya yanke shawara ne bayan ya kalli makomar PDP, ya gano cewa mafi alheri shi shi ne ya haɗe da tawagar masu son ci gaba a jam’iyyar APC.

Hon. Taribo ya ce ba shi da burin neman takara ko muƙamin siyasa face ya ƙara wa APC ƙima ta hanyar amfani da gogewarsa a siyasa.

Tsohon dan majalisar ya ce lokaci ya yi da jihar Abia za ta koma inuwa ɗaya da cibiyar siyasar kasar nan ta hanyar komawa jam’iyya mai mulki.

"Jihar Abia ta dade a tsagin 'yan adawa, kuma ba za mu iya ci gaba da zama a haka ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

"Ba addu'a ba ce": Malamin addini ya fadi abin da zai sa a samu sauki a Najeriya

Shugaban APC ya tarbe shi hannu bibbiyu

A nasa jawabin shugaban jam’iyyar APC na jihar, Dr. Kingsley Ononogbu, ya tarbi tsohon dan majalisar da hannu bibbiyu., cewar Vanguard.

A cewar shugaban, tsohon jigon jam’iyyar PDP ya yi hangen da ya kamata game da 2027 kana ya yaba masa bisa daukar matakin da ya dace a lokacin da ya dace.

PDP ta shirya kwace mulki a 2027

A wani rahoton kun ji cewa Umar Damagum ya bayar da tabbacin cewa jam'iyyar PDP na shirin dawowa kan turbar nasara a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Muƙaddashin shugaban PDP ya ba mambobin jam'iyyar hakuri kan rikicin cikin gida, inda ya ce za su karɓe mulki daga hannun APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel