Shugaban PDP Ya Faɗi Wanda Suke Son Ya Dawo Jam'iyyar Tsakanin Obi da Kwankwaso

Shugaban PDP Ya Faɗi Wanda Suke Son Ya Dawo Jam'iyyar Tsakanin Obi da Kwankwaso

  • Jam'iyyar PDP ta musanta fara tattaunawar haɗa-kai, ta nuna sha'awar Peter Obi ya jefar da LP ya dawo cikinta
  • Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya ce bayan Obi, suna shirin yadda za su dawo da mambobinsu da suka sauya sheƙa
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin Obi zai koma PDP biyo bayan ziyarar da ya kai wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Umar Damagum, mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, ya ce jam’iyyar ba ta fara tattaunawar hadewa da kowace jam'iyya ba a halin yanzu.

Damagum ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabin a cikin shirin ‘Nigeria Right Now’, na kafar talabijin na AIT, wanda aka watsa ranar 30 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Komai nisan jifa: Matashi ya shiga hannun jami'an tsaro bayan shekaru da damfara

Shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagun
Jam'iyyar PDP ta nuna tana son Peter Obi da sauran tsofaffin mambobinta su dawo gida Hoto: Umar Damagum
Asali: Twitter

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, ya kai ziyara a bayan-bayan nan ga wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP ciki har da Atiku Abubakar. 

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi zai koma PDP?

Da aka tambaye shi game da wannan ziyarar, Damagum ya ce:

"(Obi) bai kawo mun ziyara ba kuma ni ba mutum ba ne mai shisshigi da zan kama zuwa ina neman a gaya mun abin da ziyarar ta ƙunsa ba."

The Cable ta ce yayin da aka tambaye shi ko zai so Obi ya dawo PDP, shugaban jam’iyyar ya ce:

"Ba shi kadai ba, duk sauran mutanen mu da suka fita daga jam’iyyar, muna son su dawo. Kamar yadda na faɗa jam'iyyarmu tafi karfin a shafe babinta.
"Muna da isasshen wurin da zai ɗauke mu duka kuma tuni muka fara ƙoƙarin ganin mun dawo da ƴan uwanmu.

Kara karanta wannan

PDP ta watsawa Atiku ƙasa a ido kan hadaka da Kwankwaso, Obi, ta yi alfahari

"Maganar gaskiya ita ce ba a tunkare mu da zancen hadaka ba, watakila wasu ɗaiɗaiku sun fara magana kan haka amma har yau ba mu yi wata tattaunawa a matsayinmu na jam’iyya ba."

Yadda PDP za ta ɗinke ɓarakar gida

Damagum ya kuma yi magana kan rikicin jam’iyyar PDP da kuma bukatar a dakatar da wasu 'yan jam’iyyar bisa zargin cin amanar da suke yi.

Shugaban jam’iyyar PDP ya ce maimakon dakatar da su, yana ganin abin da ya fi dacewa shi ne a samu maslaha a yi sulhu. 

Wani jigon PDP a jihar Katsina ya ce duk da wahalar da mutane ke ciki, zai wahala jam'iyyar ta iya kai labari idan ba ta farka daga barci ba.

A cewarsa, babbar jam'iyyar adawa ta baro shiri tun rani amma har yanzun yana ganin tana da sauran damar da za ta iya gyara wasu kura-kuran.

A kalamansa, Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa:

Kara karanta wannan

Duk da umarnin sammaci, Ganduje ya yi biris, ya kaddamar da muhimmin aiki ga APC

"Kuskuren da PDP ta yi a 2023 yana da yawa kuma alamu sun nuna idan shugabanninmu ba su farka daga barci ba, za a sake maimaitawa ne kawai a 2027.
"Rashin haɗin kai, cin amana da son zuciya na cikin abubuwan da suka kai PDP ƙasa, ina fatan za mu gyara.
"Ko a nan Katsina ka duba Shema ya koma APC, bai kamata ana barin irinsu suna sauya sheka ba, sun yi wa jam'uyya bauta amma an yi watsi da su, dole su nemi mafita."

Jam'iyyar PDP ta shirya karɓe mulki a 2027

A wani rahoton kuma Umar Damagum ya bayar da tabbacin cewa jam'iyyar PDP na shirin dawowa kan turbar nasara a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Muƙaddashin shugaban PDP ya baiwa mambobin jam'iyyar hakuri kan rikicin cikin gida, inda ya ce za su karɓe mulki daga hannun APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel